Yadda ake ajiye giwaye a wuraren bauta a Indiya

Arjun, the caretaker, and Akila, the elephant
Bayanan hoto, Arjun, mai kula da Giwa Akila tsaye a gabanta

Sau daya a shekara, ana kwashe wasu daga giwayen da ke tsare a Indiya zuwa "sansanin kula da su", inda masu kula ke kula da su.

Omkar Khandekar ya ziyarci irin wannan wajen a jihar Tamil Nadu da ke kudancin kasar.

Bayan shekara bakwai da yin fice a kasar, giwa mai suna Akila ta san yadda ake tsayawa gaban kyamara a dauki hoton dauki da kanka.

Tana kallon kyamarar, ta daga haurenta sannan ta tsaya cak har sai kyamarar ta dauki hoton.

Ana iya gajiya, musamman idan akwai daruruwan bukatu na kowace rana.

Duk da wannan, Akila, tana gudanar da ayyukanta na yau da kullum a cikin wajen bautar Jambukeswarar.

Wadannan sun hada da masu bauta da diban ruwan da ake amfani da shi wajen wanke gumaka da kuma manyan ayyukan wuraren bauta a kewayen birni, an shirya su cikin kayan adonsu.

Da kuma hotunan dauki da kanka.

Amma a kowane watan Disamba, tana samun hutu.

"Idan mota ta shigo, ba na bukatar na ce mata ta hau motar," in ji mai kula da Akila, B Arjun. "Ba da dadewa ba, za ta kasance tare da abokanta."

Elephant
Bayanan hoto, Ana mika giwayen da ake sayar wa a Tamil Nadu zuwa sansanin kowace shekara

Indiya gida ne ga wasu giwayen daji 27,000. Ana kuma ci gaba da tsare wasu giwayen 2,500 a sassan jihohin Assam da Kerala da Rajasthan da Tamil Nadu.

An yi imanin kasar ta zama "wurin haihuwar giwaye don amfanin mutane".

'Yan India sun kama giwaye cikin shekaru aru-aru. Amma shekara 17 da suka gabata, bayan zanga-zangar da masu fafutukar kare hakkin dabbobi suka yi kan cin zarafin dabbobi da kuma rashin abinci da giwayen ke fama da shi, gwamnati ta sa baki don tausaya wa dabbobi.

Saboda haka, Akila da sauran giwaye da dama da ke tsare a wuraren bauta a Indiya yanzu an kawo su zuwa "sansanin kula da su" kowace shekara.

Cikin makwanni da dama, dabbobin sun yi birgima a cikin wani fili mai kadada shida a wani daji da ke gundumar Nilgiris, wani bangare na yanki mai tsauni da ke Yammacin Ghats.

Elephant with caretaker
Bayanan hoto, Indiya tana da sama da giwaye 2,000 da ke tsare

An bayyana sansanonin a matsayin shirin kula da lafiyar dabbobi kuma ya zama shahararren taron shekara-shekara na giwayen da ke tsare.

Akila da sauran giwaye 27 suna halartar taron wanda aka bude ranar 15 ga Disamban bara kuma taron zai ci gaba har zuwa 31 ga watan Janairu, wanda aka kashe kimanin $200,000 wajen tafiyar da shi.

Magoya baya na cewa an kashe kudi yadda ya kamata. Samun sarari daga birnin a wajen giwayen wata waraka ce, in ji S Selvaraj, jami'in kula da daji a yankin.

"Giwayen daji suna zaune a garkunan dabbobi da ke daukar dabbobi 35 amma akwai wata giwa guda a cikin wajen bauta," in ji shi.

Elephant being fed
Bayanan hoto, Ana kashe kimanin $200,000 wajen tafiyar da sansanin

Akila, mai shekara 16 ta dade a sansanin tun 2012, shekarar da aka sayar da ita ga wajen bautar. Arjun, wanda yake tare da ita duk shekara, shi ne mai kula da giwa a karni na hudu.

A sansanin, ya kan yi wa Akila wanka sau biyu a rana, yana bata wani hadin hatsi na musamman da kayan marmari da aka hada da sinadarin gina jiki na bitamin sannan kuma ya zagaya da ita.

Tawagar likitocin dabbobi suna aiki don sa ido kan lafiyar manyan baki, a lokaci guda kuma ana koya wa masu kula da su a fannoni kamar abincin giwaye da motsa jiki.

Akila ma ta kulla abota da Andal, wata tsohuwar giwa daga wani wajen bauta da ke jihar, in ji Arjun.

Amma duk da irin bishiyoyi masu inuwa, hakan ya sha ban-ban da rayuwar giwaye ta "yau da kullum".

Elephant at the camp
Bayanan hoto, Gwamnati ta kafa sansanonin bayan zanga-zangar nuna adawa da yadda masu kula da giwaye ke cin zarafin giwayen

Sansanin da ke kewaye yana da dogon gini da kuma shinge na lantarki mai nisan kilomita 1.5.

Duk da yake giwayen suna samun kulawa sosai, suna kasancewa a daure a mafi yawan lokuta sannan ana ajiye su karkashin kulawar masu kula da su.

"Giwaye sun fi dacewa da daji ba wajen bauta ba, sansanin kula da su kamar an tsare su ne tsawon rayuwarsu," in ji Sunish Subramanian, na kungiyar kula da tsirrai da dabbobi a yammacin birnin Mumbai.

"Ko a sansanin, ana kulle dabbobin kuma suna zaune ne cikin yanayi na rashin tsafta," a cewarsa.

"Idan har ya zama dole a ci gaba da al'adar, ya kamata a killace giwayen da ke zaune a wajen bautar a sansanin na tsawon shekaru - cikin yanayi mai kyau sannan a rika kai su wajen bautar kawai lokacin bukukuwa."

Elephant taking a nap
Bayanan hoto, An bayyana sansanonin a matsayin shirin kula da walwalar dabbobi

Hatta idan suna su kadai, giwayen - kamar Andal da Akila - ba a barinsu su kusanci juna.

Arjun ya bayyana cewa "Dole ne na tabbatar cewa su biyun sun nisanta da junansu - in ba haka ba, zai yi wahala a raba su idan muka koma,"

Ba wai kawai masu rajin kare hakkin dabbobi ba ne nuna damuwa ba.

Sansanin ya zama wani wajen shakatawa a shekarun baya-bayan nan, inda ya jawo hankulan baki daga kauyuka makwabta.

Mafi yawa suna zuwa su yi kallo daga dan nesa inda aka sa shinge. Amma ba kowa ba ne yake farin ciki ba a wajen sansanin.

A shekarar 2018, wata kungiyar manoma wacce ke wakiltar kauyuka 23 da ke kusa da wajen, ta gabatar da korafinta ga kotu da ta sauyawa sansanin mazauni.

Takardar korafin na ikirari cewa kanshin dabbobin - duk mata yana jawo hankalin giwaye maza daga daji.

Wannan ya sa suka ci gaba da fitowa dada daji, yawanci suna lalata amfanin gona da manoma ke dogaro da su don abinci. Kungiyar ta ce mutane 16 ne suka mutu ta irin wannan lamari.

Elephant being bathed
Bayanan hoto, Sansanin ya zama wani wajen shakatawa a shekarun baya-bayan nan

Amma kotu ta yi watsi da korafin. A maimakon haka, ta bukaci dalilin da ya sa ake da gidajen mutane a wajen da aka san na giwaye ne.

Kotun ta kuma caccaki gwamnatin jihar ta samar da sansanonin kula da giwayen.

Ta ce, "Wata rana, wannan kotu za ta hana al'adar killace giwayen a wajen bauta."

Amma Arjun ba zai iya yarda ya rabu da Akila ba.

"Ina son ta kamar mahaifiyata," in ji shi. "Tana ciyar da iyalina, kamar yadda mahaifiyata ta saba yi. Idan ba ta nan, ban san abin da zan yi ba."

Amma kuma ya fahimci cewa giwarsa za ta iya zama cikin kadaici. "Kuma wannan shi ne dalilin da yasa nake yin aiki sau biyu don na tabbatar ba ta shiga kadaici ba."

Presentational grey line

Hotuna: Omkar Khandekar