An rufe makarantun kwana a Malawi

Hukumomin yawancin makarantun kwana a Malawi sun rufe su tare da umartar dalibai su koma gida, mako guda gabannin hukuncin da kotun kasar za ta yanke kan zaben da aka yi mai cike da ta'kaddama.

Jam'iyyun adawa na kalubalantar nasarar da Shugaba Peter Mutharika ya yi a zaben da aka yi a watan Mayun bara, ita kuma kotu ta sanar da za ta yanke hukunci ranar Litinin mai zuwa.

Makarantun dai na tsoron abin da ka je ya zo bayan hukuncin kotun, wanda ka iya tayar da hargitsi.

Manyan kamfanonin motocin sufurin bas-bas sun sanar da cewa ba za su fito aiki a ranar ba.

Malawi dai ta dade tana fuskantar tashin hankalin siyasa tun bayan kammala zaben na bara.

Ministan sadarwar kasar ya yi kiran jama'a su kwantar da hankali, tare da cewa gwamnati ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama'a.