'Rikicin Boko Haram ne ya hana ni yin karatu'
Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
Ko wacce ranar 24 ga watan Janairu rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Ilimi ta Duniya, da nufin kara fito da rawar da ilimi ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kuma ci gaban al'umma.
To sai dai kuma a wasu kasashen duniya, yara masu dimbin yawa ba sa zuwa makaranta balle su samu ilimin da zai ba damar taka rawar da ta dace domin ciyar da al'umma gaba.
A Najeriya, daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a wannan jerin kamar yadda wasu alkaluma na Majalisar Dinkin Duniya suka nuna, dalilan da ke tarnaki ga cimma burin ilmantar da yara sun hada da rikice-rikicen da ke tilasta al'ummu kaurace wa muhallansu.
Albarkacin wannan rana, Salihu Adamu da Abdulbaki Jari sun rubuta mana wannan rahoton:

Da safiyar wata ranar Alhamis a watan Janairu, a unguwar Apo dake Yankin Babban Birnin Tarayya a Najeriya, wata iska mai sanyi ce ke kadawa daga gabas zuwa yamma.
A wannan lokaci yara - wasu a kasa wasu a kan ababen hawa—na ta haramar zuwa makaranta; wasu su kadai, wasu kuma manya na yi masu rakiya.
Amma a gefen babban titin da ya ratsa unguwar, akwai wani gareji inda ake gyaran motoci; a wannan tsakanin ne kuma wani yaro dan shekara 16 sanye da riga sharashara (duk da sanyin da ake yi) ke tallar ruwan leda (wanda a Turance ake kira pure water).
Yaron mai suna Muhammad Muhammad yana dauke da wani farin bokitin roba da ledojin ruwa mai yiwuwa guda 20—a kan Naira 10 ko wacce leda, Naira 200 ke nan idan ya sayar duka.
Akan bayar da sarin jakar ruwan mai leda 20 a kan Naira 100. Ke nan idan ya sayar zai samu ribar abin da bai wuce Naira 100 ba.
A cewar marikiyarsa, tura shi wannan talla abu ne da ya zama wajibi.
"A halin yanzu abin da ke gaban mu shi ne neman abin da za mu ci", inji Kaltume Muhammad.

A wasu ranakun kuma baya ga sayarda piya wata Muhammad na aikin sassabe da shara a gidajen makwabta inda ya ke 'samun na sabulu'
Muhammad na cikin fiye da yara miliyan 10 da hukumomin Najeriya suka tabbatar da cewa ba sa zuwa makarantar boko.
Wadannan bayin Allah biyu dai 'yan asalin garin Gwoza ne na jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Najeriya, kuma suna zaune ne a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke wannan unguwa ta Apo.
Daga kofar shiga sansanin, wani tarin kasa ne mai dan tudu wanda sai an tsallaka a shiga ciki.
A gefen dama kuwa, bene ne hawa uku mai rufin jan kwano wanda ba a kammala aikinshi ba.
Duk gidajen da ke wannan sansanin wadanda akalla za su kai hamsin na aro ne da aka bai wa 'yan gudun hijirar su zauna kafin wani lokaci.
A daya daga cikin gidajen ne kuma Muhammad da Kaltume suke zaune.
Mashigar gidan rufe take da wata farar leda mai kauri da kuma fadi.
Akalla mutum biyar ne ke zama a cikinsa.
"Da kyar na sha…"
A safiyar wata Litinin, Muhammad ya tafi karatu wasu mahara suka far wa makarantar da yake zuwa inda sukayi ta'adi mai yawa.
"Da farko dai sun je neman malamai ne amma sai suka samu malamai sun watse, sai suka kama dalibai, suka farfasa ofisoshi, suka kona takardu sannan suka cire tutar makarantar mu suka kafa ta su".
Muhammad ya ci gaba da cewa daga nan sai suka gudu suka bar garin zuwa wannan sansanin dake Abuja.
Kuma tun dawowar su bai kara shiga makaranta ba.
Wahala da damuwa
Malama Kaltume, sanye da dogon hijabi tana zaune a kan wata farar kujerar roba ga kuma makwabta kewaye da ita, ta bayyana dalilin da ya hana ta saka Muhammad a makaranta.
Cike da damuwa ta ce, "Wahala ce ta sa ba mu shigar da shi makaranta ba".
Ta kuma ce tun lokacin da aka far wa garinsu Gwoza suka rasa komai.
"Wurin zama ma a wannan sansani kullum kamar za a tayar da mu kuma ba mu da halin mu yi na kanmu".
Ta kara da cewa abin da ya fi kona mata rai shi ne idan taga sa'o'in Muhammad na zuwa karatu amma shi kuwa yana tafiya talla.
"Akwai wani lokaci da ya fita talla sai babur mai kafa uku ya kade shi da kyar da karo-karo muka yi mishi jinya ya samu sauki", a cewar Kaltume.
Ta ce a lokuta da dama idan yara na tafiya makaranta sai Muhammad ya yi ta kuka amma babu yadda ta iya saboda mahaifinshi ma ya shafe sama da wata uku ba su san inda yake ba.
Marikiyar ta Muhammad ta ce babban burinta a yanzu shi ne shigar da yaron makaranta da zarar ta samu dama.
"Ko yau idan na samu ko da Naira biyar ne idan har da zai iya shigar da shi makaranta da na shigar da shi".
Kason ilimi
Hukumar Raya Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNESCO, ta bayar da shawarar kasashe masu tasowa kamar Najeriya su ware akalla kashi sha biyar zuwa ashirin na kasafin kudinsu ga ilimi.
To amma tun dawowar Najeriya turbar Dimokradiyya a shekarar 1999, kasar ba ta taba ware fiye da kashi 12 cikin dari na kasafin kudinta ga bangaren ilimi ba.
Hasali ma kasafin kudin Najeriya na shekarar 2020 ya ware wa manyan ayyuka a bangaren ilimi Naira biliyan 48 ne kawai—ma'ana, bai ma kai kasha daya cikin dari ba.
Yayin wani jawabi a watannin baya, Ministan Ilimi na Najeriya Adamu Adamu ya ce akwai yara sama da miliyan 10 da ke gararamba a kan tituna maimakon zuwa makaranta a Najeriyar.
Kuma wadannan yaran sun fi yawa ne a arewacin kasar.
Masana ilimi kamar su Dokta Adamu Babikkoi na Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola na ganin cewa wadannan alkaluma 'suna tsoratarwa'.
"Duk wani mutumin da ya san abunda yakeyi wadannan alkaluma za su tayar masa da hankali sosai, sannan kuma a Najeriyar ma alkaluma sun nuna cewa kashi sittin da wani abu na wadannan yara a Arewacin kasar su ke. " inji Dokta Adamu.
Ya kuma ce tilas ne iyaye su tsaya su kwadaitar da 'ya'yansu makaranta.
Gwamnati kuwa, ta tabbatar da ta aiwatar da dukkan manufofinta kan ilimi kamar yadda ya kamata, ba wai a fada a kasa cikawa ba.
Burin Muhammad
A yanzu dai Muhammad ya ce ba shi da wani buri da ya wuce komawa makaranta, kasancewar ya bar ta ne tun da farko ala tilas.
Malama Kaltume da dan da ke gabanta na neman gwamnatoci a dukkan matakai su maida hankali ga yaran da ba sa zuwa makaranta musamman ma 'yan gudun hijira dake sansanoni daban-daban-a Najeriya.
Rikicin Boko Haram da ya daidaita yankin Arewa maso Gabashin Najeriya dai ya yi sanadiyyar raba yara da yawa da makaranta inda wasun su ke gararamba a kan tituna.
Kwararru a kan harkar ilimi dai na nuna bukatar gwamnatoci a dukkan matakai da ma masu ido da kwalli su taimaka wajen kawar da jahilci duk kuwa da cewa a hukumance karatun furamare wajibi ne kuma kyauta ne a Najeriya.












