Kamfanin NNPC ya hada kai da sojoji don dakile fasa bututun mai a Najeriya

Asalin hoton, @MKKyari
Kamfanin mai na NNPC a Najeriya zai hada kai da rundunar sojin ruwan Najeriya domin dakile ayyukan masu fasa bututun man fetur a kasar.
Babban daraktan kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara sansanin sojojin da ke Ojo a jihar Legas, inda ya gana da Rear Admiral Oladele Daji.
Kyari ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Twitter yana gode wa jami'an tsaron bisa abin da ya kira "muhimmin ci gaba" wurin yaki da fasa bututun mai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci Mele Kyari a watan Nuwamban 2019 da ya bayyana a gaban kwamiti mai kula da albarkatun man fetur domin ya yi bayani kan yadda fasa bututun mai ke karuwa a Najeriya.
Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya ce: "Wajibi ne kwamitinmu mai kula da man fetur ya gayyaci NNPC domin sanin yadda ake ciki da kuma matakan da suke dauka na tabbatar da tsaron bututun."
Ahmed Lawan ya kara da cewa za su duba yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kamfanin man.
"Wannan ma'aikatar ta biliyoyin kudi ce. Wasu mutane suke aikata hakan ba tsautsayi ba ne. Wajibi ne a dauki mataki," in ji Ahmed Lawan.





