Maduro: 'Idan Amurka ta so za mu sasanta'

A Venezuelan kuwa shugaba Nicolas Maduro ne ya yi kiran sasantawa kai tsaye da Amurka, tun da kokarin amfani da karfi dan tsige shi daga mukaminsa ya ci tura.

A wata hira da jaridar Washington Post, shugaba Maduro ya ce hawa teburin sulhu ka iya bude babin sabuwar alaka tsakanin kasashen biyu kuma kowacce ka iya nasara ciki har da babbar dama ga kamfanonin hakar mai na Amurka.

Amurkar dai na kallon jagoran 'yan adawa Juan Guido a matsayin halattacen shugaban rikon kwarya, tare da cewa duk wata tattaunawa da za a yi to dole ne a mika mulki ga mutumin da 'yan Venezuela suka zaba.

A bangare guda Mista Maduro ya ce duk irin takunkumin da Amurkar za ta kara sanyawa kasarsa komai karfinsa ba zai yi ko gizau ba wajen sauya matsayarsa.

Sabuwar rikita-rikitar siyasa ta sake barkewa a kasar Venezuela a farkon wannan watan, a daidai lokacin da aka haramtawa jagoran 'yan adawa Juan Guaido shiga majalisar dokokin kasar dan zabensa a karo na biyu.

Abokin hamayyarsa Luis Parra ya ayyana kan sa a matsayin shugaban majalisar, abin da magoya bayan Guiado suka kira kokarin juyin mulki a majalisa.