Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 170 sun mutu a hatsarin Jirgin Ukraine a Iran
Wani jirgin Ukraine Boeing-737 dauke da mutum sama da 170 ya yi hatsari a Iran.
Kungiyar agaji ta Red Crescent a Iran ta ce yana da wahala a samu wanda ya rayu.
Rahotanni sun ce jirgin ya yi hatsari ne jim kadan bayan ya tashi a tashar jirgin sama ta Imam Khomeini a Tehran.
Jirgin ya tashi ne da nufin zuwa Kyiv babbar birnin Ukraine. Gwamnatin Ukraine ta ce za ta kaddamar da bincike kan hatsarin.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce Shugaba Volodymyr Zelensky ya katse ziyarar da yake a Oman inda ya dawo Kyiv.
"Ina jajantawa 'yan uwa da abokan arziki na fasinjoji da jami'an jirgin da hatsarin ya rutsa da su," in ji sanarwar.
Babu dai tabbaci ko hatsarin na da nasaba da rikicin Iran da Amurka.
Tuni aka tura jami'an agaji zuwa inda jirgin ya yi hatsari domin bincike ko za a samu masu yawancin rai.
Kazalika, Ministan harkokin wajen Iran Vadym Prystaiko ya tabbatar da hadarin jirgin.
Ya bayyana cewa akwai 'yan Birtaniya uku da hatsarin ya rutsa da su wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 170.
Sauran 'yan kasashen da hatsarin ya rutsa da su kamar yadda ministan ya shaida sun hada da:
'Yan Canada 63
'Yan Ukraine 11, ciki har da ma'aikatan jirgin
'Yan kasar Sweden 10
'Yan Afghanistan hudu
'Yan kasar Jamus uku