An kashe hafsoshin soji 28 a harin sama

Asalin hoton, Reuters
Hafsoshin soji akalla 28 ne suka mutu a wani harin saman da aka kai wa kwalejin horas da kananan hafsojin soji a birnin Tripoli na Libya.
Ba a samu cikakken bayani game da harin ba amma rahotanni daga kasar na cewa mayakan Janar Khalifa Haftar, da ke yakar gwamnatin kasar ne suka kai harin.
An ga sassan jikkunan mutane da suka dagargaje a warwatse a kasa a cikin wasu hotuna da aka wallafa da ke nuna irin barnar da harin ya yi.
Kakanin ma'aikatar lafiyar kasar Amin al-Hashemi, ya tabbatar da mutuwar kananan hafsoshin soji 28 a harin wanda ya raunata wasu gommai a kwalejin kananan hafsoshin.
Gwamnatin Libya wadda Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya ta dade tana yakar 'yan tawayen da janar Khalifa Haftar ke jagoranta.
Rikici da rabuwar kai sun barke a kasar ne a shekarar 2011 bayan kashe shugaban kasar da ya dade yana mulki Muammar Gaddafi.
Daga lokacin kasar ta tsinci kanta cikin yakin basasa, ba tare da samun gwamnati daya mai cikakken iko da ke jagorantar kasar ba.
A watan Afrilun 2019 ne Janar Khalifa Haftar da mayakansa daga gabashin kasar suka kaddamar da fara kai hare-hare a kan gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na'am da ita, mai hedikwata a birnin Tripoli











