MDD ta tsawaita aikinta na shiga tsakani a Libya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita aikin hukumar da ke sa ido kan rikicin Libya wato UNSMIL na tsawon shekara daya saboda ta taimaka a kawo karshen yakin da ke neman mamaye dukkan sassan kasar.
Kwamitin ya nuna damuwarsa kan hare-haren da 'yan tawaye masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar ke kai wa kan birnin Trabulus.
Majalisar DD ta sake nanata kiran da tayi a baya na dukkan bangarorin su cigaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma ta fadada ayukan UNSMIL na taimakawa an cimma wannan mataki.
Jakadan MDD a Libya Ghassan Salame, ya yi gargadin cewa kasar na iya afkawa cikin yaki gaba daya wanda ka iya janyo a raba ta gida biyu na din din din.
Ya kuma ce wasu kasashen waje ne ke rura wutar rikicin saboda yadda suke ba bangarorin kayan yaki - wanda ya sabawa takunkumin da MDD ta saka wa kasar kan batun.

Asalin hoton, AFP
Jagoran 'yan tawaye, Janar Haftar na samun goyon bayan Faransa da Amurka da kuma Rasha.
Wannan kudurin na son ganin kasashen sun daina shisshigi cikin rikicin kasar.







