United ta nemi fam miliyan 150 a kan Pogba, Salisu zai je Firimiya

Manchester United ta bayyana Jack Grealish na Aston Villa da kuma James Maddison na Leicester a matsayin 'yan wasan da ke sahun gaba cikin wadanda take so ta sayo a watan Janairu kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.
Haka ma United din na son sayen Emre Can na Juventus da kuma dan wasan tsakiyar Newcastle Sean Longstaff. (ESPN).
United za ta sayar da Paul Pogba ga Real Madrid in har za ta iya biyan fam miliyan 150. (Express).
Ita kuwa Aston Villa na son sayen 'yan wasan Chelsea Michy Batshuayi da Olivier Giroud.(Sun).
Dan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang ya sanar da sha'awarsa ta ci gaba da kasancewa tare da kungiyar.(Evening Standard).
A wata mai kama da haka Arsenal na son kawo mai tsaron bayan Bournemouth Nathan Ake.(Telegraph).
Inter Milan na kan tattaunawa da wakilan Christian Eriksen na Tottenham (Sky Sports).
Manchester City za ta kara wa Fernandinho yarjejeniyar shekara daya.(Sun).
Lyon ta yi watsi da tayin fam miliyan 40 da Chelsea ta yi wa dan wasan gabanta Moussa Dembele.(Footmercato).
Southampton na shirin kawo mai tsaron bayan Ghana Mohammed Salisu da ke wasa a Valladolid da ke Sifaniya.(Sky Sports).
Ita kuwa Sheffield ta ware fam miliyan 17 don taya dan wasan Guinea da ke buga wa Olympiakos ta Girka tsakiya wato Mady Camara.(Star).
Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta duniya ta bukaci hukumomi da su shawo kan matsalar buga wasanni da a ke yi babu hutu, bayan 'yan wasa 53 sun samu raunuka wasannin Firimiyya na lokacin hutu.(Telegraph).











