Barack Obama: Mata sun fi maza ta kowanne fanni

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya na gabatar da jawabi a taron asusun Obama Foundation a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia ranar 13 ga watan Disamba 2019

Asalin hoton, European Photopress Agency

Bayanan hoto, Barack Obama
    • Marubuci, Daga Saira Asher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Singapore

Tsohon shugaban ya ce idan mata ne za su jagoranci kasashen duniya, za a samu gagarumin ci gaba ta fannoni da dama ciki har da inganta rayuwar jama'a.

Barrack Obama ya yi kalaman ne a kasar Singapore tare da jaddada ''babu tababa mata sun fi maza ta fannoni da dama''

Ya kara da cewa yawancin matsalolin da ake samu maza ke haddasa su musamman wadanda ke rike da madafun iko da manyan mukamai.

Ya kuma yi jawabi kan rarrabuwar kai da ake samu ta fuskar siyasa da amfani da shafukan sada zumunta wajen yada labaran karya.

Da ya ke jawabi a wani taro mai zaman kansa kan kyakkyawan shugabanci, Mista Obama ya ce a lokacin da ya ke shugaban Amurka ya yi tunanin yadda duniya za ta kasance idan mata ne ke jan ragamarta.

''Mata, ina son shaida muku ba ku cika tara ba, amma abin da zance shi ne kun fi mu, ina nufin mu maza ta fannoni da dama.

Ina da kwarin gwiwar, idan aka ba ku jagorancin duniya za ku kawo sauyi cikin shekara biyu. Za a samu ci gaba da inganci ta fannonin da suka dace, za ku sauya komai.''

A lokacin da aka tambaye shi ko yana sha'awar sake komawa jagorancin al'umma? Sai ya kada baki ya ce a jira a ga lokacin tukunna.

''Idan ka kalli duniya baki dayanta, da matsalolin da suka yi ma ta dabaibayi, yawanci tsofaffi ne ke haddasa su wadanda ba sa son matsa wa wasu su samu dama a wajen,'' inji Obama.

''Ya na da muhimmanci shugabannin siyasa su yi wa kansu tunatarwa, sun samu matsayin ne don yi wa al'umma aiki, ba wai kana kan kujerar domin kashin kanka, ko kara wa kanka karfin fada aji.''

Mista Obama ya jagoranci Amurka daga shekarar 2009 zuwa 20017.

Tun bayan fita daga fadar White House, shi da maidakinsa Michelle Obama suka kafa wata gidauniya da ke wayar da kan mata a fadin duniya kan kyakkyawan shugabanci.

A makon da ya gabata Obama da Michelle sun halarci wani taro da gidauniyarsu ta shirya a birnin Kuala Lampur na kasar Malaysia.