Sarki Sanusi ya amince da nadin Shugaban Majalisar Sarakuna

Asalin hoton, Getty Images
Sakin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce ya amince da nadin da gwamna Ganduje ya yi masa na shugabantar majalisar sarakuna.
Wata takarda da gwamna Ganduje ya aike wa Sarki Sanusi ranar 19 ga Disamba ta nemi Sarki Sanusin da ko dai ya bayyana amincewarsa da nadin ko kuma ya yi watsi da shi.
Katsam kuma a wata wasikar mai dauke da sa hannun sakataren Sarkin Kano, Abba Yusuf da fadar ta aike wa gwamna Ganduje, ta ce Sarki Sanusi ya karbi nadin da gwamna ya yi masa.
Sai dai Sarki Sanusin ya ce "yana neman karin bayani daga wurin gwamna dangane da nadin sauran 'yan majalisar da ofishin majalisar da ma'aikatan majalisa da kuma dukkanin abubuwan da ake bukata domin gudanar da majalisar."
Duk da cewa BBC ba ta samu ji daga fadar Kano ba kan takardar, wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar ya tabbatar wa BBC karbar kofin takardar.





















