Yadda aka yi bikin 'sauya sunan yaro daga Buhari' a Katsina
Latsa wannan alamar lasifikar domin jin dalilan da ya sa Babangida Ibrahim sauya wa dansa sun:
A karshen mako ne dai aka yi wani bikin sauya sunan wani yaro dan shekara hudu da haihuwa, a jihar Katsina, lamarin da yake matukar jan hankalin 'yan Najeriya.
Mahaifin yaron ya sauya sunan dan nasa mai suna Buhari zuwa Sulaiman saboda a cewarsa mai asalin sunan yana da tausayi ba kawai mutanen da yake jagoranta ba, har ma dabbobin da ke karkashin mulkinsa.
Bikin na zuwa ne, mako guda bayan wani makamancinsa da aka yi a Kano, wanda wani magidanci ya sauya sunansa daga Muhammmadu Ibrahim zuwa Muhammadu Buhari.









