Bosnia za ta dawo da dalibai 'yan Najeriya da ta kama

'Yan gudun hijira ba a bisa ka'ida ba

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomi a kasar Bosnia sun shaida wa BBC cewa kwanan nan za a mayar da wasu dalibai biyu 'yan Najeriya da suka ce an kai su Bosnia daga kasar Croatia ba a bisa ka'ida ba, gida.

Daliban da suka je wata gasar kwallon teburi ta jami'o'i a Croatia sun ce an dauka su 'yan gudun hijira ne ba a bisa ka'ida ba.

Ma'aikatar tsaron Bosnia ta ce za a koma da daliban gida Najeriya kwanan nan, amma ba ta bayyana takamaiman lokaci ba.

A cewar dalibai Alexandro Abia da Kenneth Eboh, suna tafe ne a Zagreb a tsakiyar watan Nuwamba lokacin da 'yan sanda suka kama su suka kai su caji ofis.

Bayan da aka gama yi masu tambayoyi, sun bayyana cewa an dauke su a wata mota an kai su kan iyaka sannan aka nuna masu bindiga aka ce su taka har Bosnia.

Sun ce hukumomin Croatia ba su ba su damar komawa otal dinsu don daukar fasfo dinsu ba mai dauke da bizarsu.

Gwamnatin Croatia ta musanta hakan, inda ta ce daliban sun bace ne bayan da suka kwashe kayansu daga otal din da suka sauka.

Mista Abia da Mista Eboh sun ce tun isarsu Bosnia sama da mako uku da ya wuce, an kai su sansanonin 'yan gudun hijira biyu kuma sun bayyana cewa sansanonin na cikin mummunan yanayi.