Ya kamata Garba Shehu ya ajiye aikinsa – Aisha Buhari

Aisha Buhari

Asalin hoton, @aishamBuhari

Bayanan hoto, Aisha ta nuna takaici kan yadda ta ce "Garba Shehu ke kware wa Buhari baya"
Lokacin karatu: Minti 3

Mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha ta ce ya kamata hadimin shugaban kan yada labarai Garba Shehu ya ajiye mukaminsa saboda gazawa wurin gudanar da aikinsa.

A wani sakon da ta wallafa mai taken "Garba Shehu na wuce gona da iri", mai dakin Shugaba Buharin ta nuna yadda ta ce mai magana da yawun mijin nata ke wuce gona da iri da kuma 'yi wa iyalan shugaban shisshigi da zagon kasa'.

Aisha Buhari ta nuna takaici bisa yadda ta ce Garba Shehu ke kware wa Buhari baya, kasancewarsa yaron wasu miyagu.

Ta kuma koka bisa yadda wani lokaci a kan samu abin magana da ke shafar ta da kuma Shugaba Muhammadu Buhari, har a yi ta tseguntawa a bakin duniya, amma Garba Shehu ba ya tsayawa ya kare martabarsu a lokutan da bukatar hakan kan taso.

Da take cewa ba za ta lamunci halayyar Garba Shehun ba, Aisha Buhari ta ce ya taba cewa ba zai taba bari ofishinta ya yi aiki ba, kuma ya shaida wa hadimansa cewa Mamman Daura ne ya sa shi fadin hakan.

A cewarta, fuska biyu da Garba Shehu yake yi da irin zubewar mutuncin da ya jawo wa fadar gwamnati da iyalan shugaban kasar ya sa yanzu ita da iyalanta ba su aminta da shi ba. Ta kara da cewa a wuraren da aka san abin da ya dace, kamata ya yi Garba Shehun ya ajiye aikinsa.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Uwar gidan shugaban kasar ta kara da zargin cewa Garba Shehu ya fi karkata ga wasu da ta yi shaguben kiran su masu shisshigi ga harkokin iyalan shugaban kasa. Ta bayyana mutanen a matsayin masu ikon-boye a fadar shugaban kasar, duk da cewa ba zababbu ba ne.

Ta yi misali da dambarawar da aka yi a fadar shugaban kasar, wadda aka yada a wani hoton bidiyo, wanda a ciki take kumfar-baki cewa an rufe mata kofa a kofar wani gida da ke fadar, tana neman mutanen da ke ciki, wadanda ta tabbatar da cewa iyalin dan'uwan Shugaba Buhari ne, wato Mamman Daura da su bude mata kofa!

Aisha Buhari ta ce an jirkita labarin da karerayi amma Garba Shehu bai fito ya gyara maganar ba. Tana cewa wannan butulci ne.

Duk da cewa ba ta fito fili ta ambaci maganar auren da aka yi ta yayatawa ta kafafen intanet ba cewa, Shugaba Buhari zai auri wata minista ba, maidakin nasa ta ce Garba Shehu bai yi komai ba wajen kashe maganar ko fayyace gaskiyar al`amarin, duk da cewa aikinsa ne kare martabar fadar shugaban kasa da kayan fadar.

Short presentational grey line

Zuwa yanzu dai mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labaran bai ce komai a kan wannan zargin ba.

Amma wasu masu lura da al`amura na ganin cewa watakila ta yi abin nan ne da `yan magana kan ce Zomo ba ya fushi da makashinsa, sai maratayi! Ko fushin kaza huce kan dami.

Wasu na ganin cewa ba Garba Shehu, ne kadai ke da alhakin kare martabar gwamnatin shugaba Buhari ta fuskar yada labarai ba.

Suna cewa akwai mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai, wato Femi Adeshina, da kuma Ministan yada labarai, Lai Mohammed, wadanda duka suna gaba da Garba Shehu a tsarin aiki. Amma ba ta ga gazawarsu ba, sai ta Garba Shehu. Don haka ne ma wasu ke ganin cewa da walakin, wai goro a miya!

Wannan dai ba shi ne karon farko da Maidakin shugaban kasar ke takun-saka da mukarraban Shugaba Buhari ba. Ko a shekara ta 2016, tun Shugaba Buhari bai yi nisa da jan-zaren wa`adin mulkinsa na farko ba, a wata hira da BBC, Aisha Buhari ta caccaki wasu da ta ce sun kakkange shugaban kasar, sun kuma yi kane-kane a babban gidan.

Ta ce mutanen ba sa nufin gwamnatinsa da alheri, har ma ta yi fargabar cewa idan shugaban kasar bai sauya salo ba, to da wuya ya kai labari a babban zaben kasar da aka yi a farkon wannan shekarar!