Mata 5 da suka yi fice a kare hakkin bil-Adama a arewacin Najeriya

Laila Dogonyaro

Asalin hoton, Isa Dogonyaro

Bayanan hoto, An haifi Laila Dogonyaro a birnin Kano a shekarar 1944

Sau da yawa fafutukar kare hakkokin bil-Adam da fafutukar kare hakkokin mata kan yi kama sosai musamman idan masu fafutukar mata ne.

Me ya sa ake bikin Ranar Kare Hakkin Bil-Adama a rana irin ta yau - 10 ga watan Disamba - kuma mene ne muhimmancinta ga mata?

A wannan rana ce a shekarar 1948 aka amince da Kundin Ayyana Hakkokin Bil-Adama, wanda a ciki aka fayyace hakkin da ko wane dan-Adam ke da shi da ba za a tauye masa ba.

Kundin ya fayyace karara cewa kar a take hakki ta hanyar la'akari da bambancin asali, ko launin fata, ko addini, ko jinsi, ko siyasa, ko wani ra'ayi na daban, ko kasa, ko wadata, ko haihuwa, ko wani matsayi a al'umma.

Eleanor Roosevelt, matar Shugaba Franklin Delano Roosevelt na Amurka, ta shiga tarihi saboda muhimmiyar rawar da ta taka - a matsayinta na shugabar kwamitin shirya kundin - wajen hada wannan kundi na hakkokin bil-Adama.

Mata biyar suka yi fice wajen kare hakkin bil-Adama a arewacin Najeriya

Mun duba rayuwar wasu mata biyar da suka yi fice wurin kare hakkokin bil-Adam a arewacin Najeriya.

Saboda taken wannan rana a bana shi ne: "Matasan da suka yi tsayin-daka domin kare hakkokin bil-Adam", biyu daga cikin matan da muka duba matasa ne.

Laila Dogonyaro

Laila Dogonyaro

Asalin hoton, Isa Dogonyaro

Bayanan hoto, Laila Dogonyaro

An dai haife ta ne a birnin Kano a 1944, aka yi mata aure tana da shekara 13. Ta rasu tana da shekara 66 a shekarar 2011.

Hajiya Laila Dogonyaro ta shahara wurin fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilimantar da su.

Ta shugabanci Majalisar Kasa ta Kungiyoyin Mata a Najeriya, wato National Council of Women's Societies (NCWS) daga 1993 zuwa 1995.

Kafin haka, tana cikin matan da suka kirkiri Jam'iyyar Matan Arewa da nufin taimaka wa iyalai matalauta a arewacin Najeriya.

Hafsat Baba

Hafsat Baba

Asalin hoton, Hafsat Baba

Bayanan hoto, Hafsat Baba

An haife ta ne a 1957, kuma ta shahara wajen fafutukar kare hakkokin mata, musamman wadanda mazajensu suka mutu da kananan yara, musamman marayu.

Hajiya Hafsat Baba ce Kwamishinar Kula da Ayyukan Jinkai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna. Kafin nan kuma ta rike mukamin Kwamishinar Mata.

Ita ma dai ta taka rawa a Jam'iyyar Matan Arewa, inda ta rike mukamin mai kula da ayyuka a Jihar Kaduna daga 2002 zuwa 2006 da Majalisar Kungiyoyin Mata ta Kasa, inda ta jagoranci harkar bincike a Jihar Kaduna daga 2006 zuwa 2010.

Saudatu Mahadi

Saudatu Mahadi

Asalin hoton, WRAPA

Hajiya Saudatu Mahdi ce ke jagorantar kungiyar WRAPA (Women's Rights Advancement & Protection Alternative, a Turance) mai fafutukar kare hakkokin mata da kwato masu 'yancinsu a Najeriya.

Ta taba zama mamba a majalisar gudanarwar Hukumar Kare Hakkin Bil-Adama ta Kasa a Najeriya, sannan kuma tana cikin matan da suka assasa yekuwar nan ta Bring Back Our Girls da nufin zaburar da hukumomi su ceto ''yan matan Chibok da ''yan Boko Haram suka sace.

A shekarar 2011 aka ba ta lambar yabo ta kasa ta MFR.

Maryam Awaisu

Maryam Awaisu

Asalin hoton, WITTER/STEVESCOTT_ITV

Bayanan hoto, Maryam Awaisu

Maryam Awaisu marubuciya ce, kuma mai fafutukar kare hakkin mata.

Tana cikin matasan matan da suka assasa yekuwar #ArewaMeToo, wadda ke karfafa gwiwar wadanda aka taba yi wa fyade su fito su fada domin a dauki mataki.

Sakamakon wannan fafutuka ne ma jami'an tsaro suka kama ta a harabar ofishinta, ko da yake sun sake ta daga bisani.

Hassana Maina

Hassana Maina

Asalin hoton, Hassana Maina

Bayanan hoto, Hassana Maina

Hassana Maina ta karanci aikin lauya a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria.

'Yar Shekara 21 da haihuwa, ita ce jagorar fafutukar nan ta #NorthNormal mai burin ganin jihohin Najeriya sun shigar da dokar haramta cin zarafin jama'a cikin kundin dokokinsu.

A yanzu haka tana jagorantar wani shiri na wayar da kan yara 'yan makaranta game da cin zarafi ta hanyar lalata.

Presentational grey line

Bayan Eleanor Roosevelt, wadansu matan ma sun taka rawa, musamman wurin ganin an shigar da hakkokin mata cikin kundin.

Wadannan mata sun hada da Hansa Mehta (wata mai fafutukar kare hakkokin mata 'yar Indiya), da Minerva Bernardino (wata ''yar Jamhuriyar Dominica wacce ta tsaya kai-da-fata a kan sai an saka "daidaito tsakanin mata da maza" a shimfidar kundin).

Akwai kuma Shaista Ikramullah (wata 'yar Pakistan da ta taka rawa wajen ganin an bayar da fifiko ga 'yanci da daidato da kuma damar zabi a cikin kundin).

Sai Bodil Begtrup ('yar Denmark din da ta nace a ambaci "kowa" ko "ko wane bil-Adama" a maimakon "ko wane mutum") da Marie-Hélène Lefaucheux (wata Bafaranshiya da ta yi fafutukar ganin an saka kawar da bambancin jinsi a kundin).

Akwai kuma Evdokia Uralova (wata 'yar Jamhuriyar Byelorussia - wadda a wancan lokacin take karkashin Tarayyar Soviet - da ta jajirce wajen ganin an saka batun bai wa mata da maza albashi daidai wa daida idan suka yi aiki iri daya),

Da kuma Lakshmi Menon ('yar Indiya da ta bukaci a ambaci "hakkoki iri daya na maza da mata", da kuma tabbatar da cewa hakkokin na kowa da kowa ne lokacin da aka yi yunkurin kebe mutanen da ke karkashin mulkin mallaka a zamanin.