Za mu rinka kiran Buhari mai kama-karya - Punch

Masu sharhi kan al'amura a Najeriya na ganin da walakin dangane da yadda kafafen watsa labaran kasar ke caccakar gwamnatin Shugaba Buhari.
A ranar Laraba ne dai jaridar Punch a kasar ta buga wani labari inda ta sanar da fara bayyana Shugaba Buhari da shugaban kama-karya kuma na mulkin soja.
Mannir Dan Ali, shugaban gidan jaridar Media Trust ya ce idan dukkanin bangarorin biyu na zartarwa da na jarida za su gudanar da ayyukan bisa ka'ida to za a zauna lafiya da juna.
Latsa wannan alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron Mannir Dan Ali

Me ya faru?
Jaridar ta Punch a dab'inta na ranar Larabar nan 11 ga watan Disamba mai taken "Buhari's Lawlessness; Our Stand" ta ce ta yanke shawarar daga yanzu za ta rinka makala wa Shugaba Buhari lakabin soja na Manjo Janar da kuma bayyana salon mulkinsa da na kama-karya.
Jaridar ta ce ta yanke wannan shawara ne saboda lura da irin 'keta hakkokin dan adam' da Shugaba Buharin yake yi a kasar, al'amarin da jaridar ta ce ya sha ban-ban da salon mulkin dimokradiyya.
"A wani matakin nuna rashin amincewarmu ga salon mulkin kama-karya da na soja, Punch ( a dukkan shafukanta na jarida da intanet da wasanni da daba'in ranar Asabar da na Lahadi) daga yanzu za ta fara makala wa Buhari tsohon matsayinsa na soja na Manjo Janar wanda yake amfani da shi lokacin mulkin soja a shekarun 1980s.
Sannan kuma za mu rinka bayyana gwamnatinsa da ta danniya, har zuwa lokacin da ya fara mutunta dokokin kasa."
Punch ta zayyana wasu dalilanta da ta ce su ne suka ba ta damar ayyana gwamnatin Shugaba Buhari da 'kama-karya' da 'rashin mutunta doka da oda', kamar haka;
- Batun "kama dan jaridar nan na SaharaReporters, Omoyele Sowore da jami'an hukumar SSS aka ce sun yi a cikin kotu.
- Yadda 'yan jaridu suke fuskantar kalubalen fadin albarkacin bakinsu.
- Kokarin hana jama'a fadin albarkacin bakinsu a soshiyal midiya.
- Kamawa da tsare 'yan kasa fiye da awa 48 da jami'an tsaron kasar ke yi karkashin gwamnatin Buhari.
- Yadda gwamnatin Buhari ke ci gaba da tsare tsohon mai bai wa shugaban kasa Jonathan shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki da jagoran kungiyar IMN da gwamnati ta haramta, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
- Irin yadda jami'an SSS suka yi wa alkalai dirar mikiya a gwamnatin Buhari."

Martanin fadar shugaban kasa
Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa "jaridar Punch ta koma jaridar siyasa".
Ya kara da cewa "jaridar na magana ne kan kama Omoyele Sowore wanda shi kuma ya yi kira da a yi juyin juya-hali bayan da ya fadi daga zaben shugaban kasa.
Saboda haka shi Omoyele Sowore dan siyasa ne ba dan jarida ba."
Dangane kuma da batun kiran Buhari shugaban "kama-karya", Malam Garba Shehu ya ce "dokar Najeriya ce ta bayar da damar kiran Buhari Shugaba."
"Babu wani matakin doka da za mu dauka illa dai mu bar su da 'yan Najeriya su yi hukunci, tunda sune suka zabi shugaba Buhari har karo biyu."
A kwanakin baya ne dai fadar shugaban na Najeriya ta kori dan jaridar Punch mai aika rahoto daga fadar.
Sai dai bayanai sun nuna cewa daga baya fadar ta nemi jaridar ta mayar da ma'aikacin nata amma jaridar ta Punch ta nemi Buhari ya nemi gafararta kafin ta yadda da komawar dan jaridar fadar ta gwamnati.












