Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu 'yan Najeriya sun kai wa Amaechi hari a Madrid
Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya ce wasu 'yan Najeriya sun kai masa hari a birnin Madrid.
Sakon da ya wallafa a Twitter, tsohon gwamnan na Rivers ya ce an kai masa harin ne yayin da yake halartar taron sauyin yanayi da ake gudanarwa a birnin Madrid na Spain.
Ya ce 'yan sandan Madrid ne suka tarwatsa 'yan Najeriya kafin su yi masa rauni.
"Ban ji rauni ba, na gode da goyon bayanku da kuma addu'arku," kamar yadda ministan ya wallafa a Twitter.
Bidiyon yadda 'yan Najeriyar suka kai wa ministan hari ya mamaye kafofin sada zumunta na intanet.
Wasu jaridun Najeriya sun ambato kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra tana ikirarin cewa mambobinta ne suka kai wa Amaechi hari a Spain.
Kuma kungiyar ta ce za ta ci gaba da kai 'yan siyasa hari a duk lokacin da suka yi katari da su a kasashen duniya.