Manyan matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya

Asalin hoton, @BashirAhmaad
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Matsalar tsaro a Najeriya ta dade tana ci wa kasar tuwo a kwarya. Tana kuma daga cikin manyan matsalolin da suke yi wa kasar tarnaki ta fannin ci gaba.
Daya daga cikin manyan matsalolin tsaro a Najeriya akwai matsalar kungiyar Boko Haram. Sai dai ko a kwanakin baya Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an samu sauki dangane da ayyukan kungiyar ta Boko Haram, inda ya ce an karya lagon 'yan kungiyar.
Amma jerin wasu manyan matsalolin tsaro da gwamnatin kasar ta fitar na nuna alama har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Gwamnatin kasar ta fitar da jerin matsalolin ne a cikin kundin manufofin tsaron kasar wanda shugaban ya kaddamar a ranar Laraba, 4 ga watan Disambar 2019.
Manyan matsalolin da shugaban ya ayyana sun hada da:
- Ta'addanci.
- Tsattsauran ra'ayin addini.
- Garkuwa da mutane.
- Fashi da makami.
Sauran matsalolin da suka addabi kasar sun hada da:
- Rikicin manoma da makiyaya.
- Masu tayar da kayar baya.
- 'Yan aware masu fafutukar ballewa daga kasar.
- Masu fashi a teku.
- Saukin shige da fice ta iyakokin kasar.
- Laifukan da ake yi ta intanet.
- Rikice-rikicen siyasa da na zamantakewa.
Shugaban wanda ya bayyana cewa matsalolin da ke barazana ga tsaron kasar suna da yawa ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin zamani domin magance su.
Kundin manufofin tsaro na kasar ya nuna cewa an samu galaba kan Boko Haram, amma akwai bukatar amfani da hanyoyi na zamani domin wargaza dangantakar da ke tsakanin kungiyar da kuma kungiyar ISWAP.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa suka zama barazana?
Kungiyar Boko Haram ita ce kungiyar da ta yi kaurin suna wadda gwamnatin Najeriya da sauran kasashe suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Kungiyar ta fara kai manyan hare-hare ne a Najeriya a 2009 bayan kashe shugabanta wato Muhammad Yusuf. Har yanzu gwamnatin kasar na nan tana fafatawa da kungiyar ta Boko Haram.
Matsalar Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na daga cikin manyan matsalolin tsaro a Najeriya, ta yadda a kwanakin baya wasu ke kwatanta girmar matsalar da ta Boko Haram.
Masu Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun kwana biyu suna cin karensu babu babbaka a jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da wasu jihohin da ba a rasa ba a Najeriyar.
Wannan matsala ta haramta wa mutane da dama bin hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda yawancin mutane suka koma bin jirgin kasa domin kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane.
A bangaren rikicin manoma da makiyaya, gwamnatin kasar ta dade tana fama da wannan matsalar, duk da cewa masu sharhi kan al'amuran tsaro na ganin an samu sauki ta wannan bangaren.

Asalin hoton, TWITTER/NIGERIAN ARMY
A shekarun baya an samu rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohi irinsu Benue da Nasarawa da Zamfara. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar jama'a da dama, baya ga asarar dukiyoyi.
A kudancin kasar kuma akwai 'yan tayar da kayar baya na yankin Niger Delta wadanda ake zargi da yawan fasa bututun mai da tayar da zaune tsaye a wasu sassa na yankin.
Ko a kwanakin baya sai da rundunar sojojin kasar ta kaddamar da wani atisaye da ake kira ''Operation Crocodile Smile'' a yankin kudu maso kudancin kasar, domin tabbatar da tsaro a yankin.
A wani bangaren kuma, masana tsaro da dama a Najeriya sun sha kokawa a kan yadda iyakokin kasar na kan tudu suka zama sakaka. Ana zargin hakan ya ba da dama ga batagarin da ke fasakwaurin makamai da da miyagun kwayoyi zuwa cikin kasar.
Sai dai a kwanakin baya gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani atisayen mai suna 'SWIFT RESPONSE' a matsayin daya daga cikin matakan da ta dauka na tsaftace iyakokin kasar.
Atisayen dai na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar kwastam da ta shige da fice da rundunar sojojin kasar da 'yan sanda da kuma sauran hukumomin kasar masu kayan sarki.











