DSS ta saki Omoyele Sowore

Asalin hoton, Sowore
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta saki Omoyele Sowore bayan ya yi fiye da wata uku a hannunta, kamar yadda lauyansa Femi Falana ya tabbatar wa da BBC.
Tun da farko dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin yin hakan a ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa'a 24 tare da biyansa diyyar naira ₦100,000.
Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.
Har ila yau ta ce ba zai yiwu hukumar DSS ta mayar da kanta kamar kotu ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin abokin shari'ar Sowore mai suna Olawale Bakare.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar DSS ta ce ta tsare Sowore ne saboda zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon kiran juyin juya hali da ya yi - ya yi masa lakabi da #RevolutionNow.
Omoyele Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a intanet.
Daga cikin laifukan da ake zarginsa da su har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta.







