DSS ta sake kama Sowore

Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da wasu makwabtansu a yau.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Ghana, An ci tarar kamfanin MTN

    Hukumar sadarwa ta Ghana, NCA, ta ci tarar kamfanin sadarwa na MTN Ghana.

    Hakan ya biyo bayan rashin bin umarnin da aka ba kamfanin ne bayan matsalolin da kamfanin wayar salular ya samu dangane da biyan bukatar masu amfani da layin wayarsu.

    A cikin wata wasikar da hukumar sadarwar kasar ta mikawa kamfanin sadarwa na MTN Ghana a jiya, ta bayyana damuwarta kan lamaarin ta kuma umarci kamfanin da ya mayarwa kwastamomin sa kudaden da suka yi asara.

  2. Kenya, Gini mai hawa shida ya rushe a Nairobi

    Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu bayan da wani gini mai hawa shida ya rushe a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

    Ana fargabar akwai mutane da yawa da suka makale a cikin baraguzan ginin sakamakon muryoyinsu da masu aikin ceto suka ce sun ji a lokacin da suke aikin ceton.

    Kawo yanzu dai an ceto mutum 9 daga cikin baraguzan ginin kuma ana jiyo muryar wasu da ake kokarin cetowa.

    Building Collapse

    Asalin hoton, AFP

    Building Collapse

    Asalin hoton, Dickson Omari

    Building Collapse

    Asalin hoton, Dickson Omari

  3. Gabon, An nada dan Shugaban Gabon 'mai kula da harkokin shugaban kasa'

    Gabonese president

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Ali Bongo da dansa Noureddin Bongo Valentin

    An nada babban dan Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba mai kula da harkokin shugaban kasa.

    Mukamin na Noureddin Bongo Valentin ya kunshi "taimakawa shugaban kasar kuma mahaifinsa kan duk wani abu da ya shafi kasar".

    Rahotanni sun nuna cewa an kirkiri sabon mukamin ne musamman don Noureddin a karshen taron majalisar zartarwa.

    A farkon watan Nuwamba gabon ta kaddamar da sakon tsarin yaki da cin hanci da rashawa wanda ya yi dai-dai da lokacin da Shugaba Bongo ya samu lafiya kuma ya tabbatar da an kama manyan abokansa.

  4. Burkina Faso, Shugaban Burkina Faso ya amsa kiran Macron

    Shugaban Burkina Faso, Roch Kabore ya ce zai bayar da amsa game da kiran da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi masa don tattauna batutuwan da suka shafi dakarun Barkhane.

    Ya kara da cewa taron "wata dama ce ta magana kan yakin da muke yi da ta'addanci."

    Ran 4 ga watan Disamba ne Shugaba Macron ya kira shugabannin kasashen kungiyar G5 Sahel don taro a Faransa ran 16 ga watan na Disamba.

    Kasashen G5 Sahel sun hada da Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi da Mauritania kuma suna fama da yaduwar masu ikirarin jihadi da ke da alaka da al-Qaeda da IS.

  5. An dawo da 'yan ci ranin Najeriya 168 daga Libya

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta yi amshi wasu 'yan Najeriya 168 da suka makale a Libya.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Mukaddashin shugaban NEMA na jihar Legas, Ibrahim Farinloye ya tarbi mutanen a madadin Shugaban hukumar NEMA na kasa a filin jirgin sama na Murtala Muhammaed da ke Legas.

    Mista farinloye ya shaida wa manema labarai cewa mutanen sun dawo Najeriya ne a cikin jirgin Al Buraq da aka yi masu shata.

    Jaridar ta ruwaito cewa cikin mutanen akwai 38 mata ne manya da yara mata tare da manya maza 109 da yara maza 6 da jarirai 10.

    Ya ce wannan ya kawo yawan mutanen da suka dawo daga Libya daga watan afrilun 2017 zuwa yanzu, maza 8,096 da mata 5,788.

  6. DSS ta sake kama Sowore

    A

    Asalin hoton, Sowore

    Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta sake kama Omoyele Sowore kwana daya bayan ta sake shi.

    Wakiliyar BBC ta shaida cewa jami'an DSS sun kama Mista Sowore ne bayan da ya bayyana a gaban kotu a Abuja don ci gaba da sauraren kararsa a ranar Juma'a.

    Jami'an sun yi kokarin kama shi tun a cikin kotun, bayan da alkalin da ke sauraren karar ta dage zaman zuwa 11 ga watan Fabrairun 2020 amma sai ya tirje.

    Daga nan sai ya fita wajen kotun kuma a nan ne DSS din ta kama Mista Sowore.

    An tafi da Mista Sowore a cikin motar lauyansa ne Femi Falana SAN inda jami'in DSS ke tuka motar kuma lauyan nasa ya yi mata rakiya.

    Rahotanni sun nuna cewa Alkalin ta tsere daga harabar kotun.

    Tun da farko dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin yin hakan ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa'a 24 tare da biyansa diyyar naira ₦100,000.

    Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin sakinsa ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

    Sowore
    Bayanan hoto, Sowore lokacin da ya bayyana a gaban kotu a Abuja ranar Juma'a.
  7. DSS ta yi yunkurin 'sake kama' Sowore

    Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta yunkurin sake kama Omoyele Sowore bayan ta sake shi a jiya Alhamis, kamar yadda lauyansa Femi Falana ya tabbatar wa BBC.

    An yi yunkurin kama Mista Sowore ne yayin da ya bayyana a harabar kotun da ake ci gaba da yi masa shar'ia a ranar Juma'a, kamar yadda kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta bayyana.

    Tun da farko dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin yin hakan a ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa'a 24 tare da biyansa diyyar naira ₦100,000.

    Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

    Har ila yau ta ce ba zai yiwu hukumar DSS ta mayar da kanta kamar kotu ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin abokin shari'ar Sowore mai suna Olawale Bakare.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Cardi B na son cin dafa-dukar shinkafar Najeriya

    Shahararriyar mawakiyar nan ta kasar Amurka Cardi B ta iso Najeriya don halartar wani bikin wake-wake a karshen wannan makon.

    Mawakiyar ta sanar da isowarta Najeriya ne a shafinta na Instagram, sannan ta bayyana zakuwarta da farin cikinta na zuwa nahiyar Afirka a karon farko.

    Isowarta kasar ke da wuya Cardi B ta wallafa wani bidiyo a 'story' dinta na shafin Instagram inda ta ce tana so ta fita ta yi yawon bude ido a Legas sannan kuma ta ci 'Jollof Rice' wato shinkafa dafa-duka.

    Daga muryarta da yanayin kalamanta dai ana iya gane cewa lallai Cardi B na cike da nishadi da dokin zuwa Najeriya.

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

    Ta wallafa wani bidiyo tana rawar wakar mawakin Najeriyan nan Davido wanda ta rera wasu baitoci a ciki, a lokacin da take hanyarta ta isowa Najeriyar.

  9. EFCC ta kama wani malami kan zamba

    Hukumar EFCC a jihar Kaduna ta kama wani Malam Abdulrashid Imam kan zargin zambatar wani mutum mai suna Arc Mohammed Dewu, naira miliyan uku da kuma dala dubu 24.

    Arc Mohammed Dewu ya kai karar AbdilRashid ne a watan October 2019,inda ya zarge shi da karbar kudi a hannunsa da sunan sa masa Ilimin Al-Qur'ani a cikin kansa ta hanyar amfani da aljanu.

    Mohammed Dewu ya ce Abdulrashid ya karbi kudin ne don sayen turaruka da wayoyi da zuma da za a yi aiki da su wajen 'zuba' masa ilimin a cikin kwakwalwarsa. .

  10. Masu bibiyarmu Assalamu Alaikum!

    Ku kasance da mu a wannan shafin domin karanta labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Ghana da Nijar da Kamuru da Chadi da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da su.

  11. Ban kwana

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.

    Ku duba kasa domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta a yau Alhamis zuwa yanzu da muke rufewa.

    Za ku iya ci gaba da karanta sauran labarai a sauran shafukanmu.

    Muna kara gode maku da kasancewa tare da mu.

  12. Kyanda ta kashe sama da mutane 50,000 a Afirka

    Akalla mutane 140,000 ne ciwon kyanda ya kashe a kamarin da cutar ta kara yi a duniya.

    Afrika ce ta fi yawan mamatan da mutane 52.600 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ambata.

    Ana dai iya kauce wa wannan cuta ta hanyar allurar riga-kafi. Sai dai an sami rashin cigaban allurar a cikin shekara goma a duk fadin duniya.

  13. Mawakiya Cardi B na kan hanyar zuwa Najeriya

    Cardi B

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Cardi B ta lashe kyautuka da dama ciki har da Grammy

    Shahararriyar mawakiya 'yar Amurka Cardi B tana kan hanyarta ta zuwa nahiyar Afirka a karon farko, inda za ta yi wasa a wurin bikin Livespot X Festival da zai gudana a jihar Legas.

    Belcalis Almanzar, wadda aka fi sani da Cradi B ta wallafa a Instagram: "1:03am drop my KK in NY on my way to Afrriiiiicaaaaaaaaaa baybeeeee!!!!!!."

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

    A watan da ya gaba ne ta bayar da sanarwar cewa za ta zo Najeriya domin yin wasa a Legas.

    Za ta yi casun ne a wurin bikin na kwana biyu tare da taurarin mawakan Afirka daga Ghana da Najeriya, irin su Tiwa Savage da Shata Wale da R2bees da sauransu.

    Bikin zai gudana a ranakun Asabar da Lahadi.

  14. A saki Sowore, a ba shi dubu ₦100 – Kotu ta umarci DSS

    Omoyele Sowore

    Asalin hoton, @YeleSowore

    Bayanan hoto, Daga cikin laifukan da ake zarginsa har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta

    Mai Shari'a Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin a ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa'a 24 tare da biyansa naira ₦100,000.

    Mai shari'ar ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

    Misis Ojukwu ta ce ba zai yiwu hukumar DSS ta mayar da kanta kamar kotu ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin abokin shari'ar Sowore wato Olawale Bakare.

    Kazalika ta dage sauraron karar har zuwa 6 ga watan Disamba.

    DSS tana tsare da Sowore bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon kiran juyin juya hali da ya yi - ya yi masa lakabi da Revolution Now.

    Omoyele Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a intanet.

    Daga cikin laifukan da ake zarginsa da su har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta.

  15. Majalisar Dattawa ta amince da dokar kasafin kudi ta 2020

    Sanatoci a Najeriya

    Asalin hoton, @NGRSenate

    Majalisar Dattijai a Najeriya ta sa hannu kan dokar kasafin kudi ta 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10.59.

    Majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya ce yaba wa abokan aikinsa kan kokarin da suka yi wajen tabbatar da cewa sun gyara tsarin kaddamar da kasafin kudi ta yadda zai kasance duk karshen shekara.

    A baya dai majalisar kan dauki sama da wata hudu kafin kammala muhawara tare da amincewa da kasafin kudin.

    Ahmed Lawan ya ce da ma dai wannan na daya daga cikin abubuwan da suka ci alwashin yi a majalisa ta tara.

    Ya kuma yi wa bangaren zartaswa fatan alheri da fatan gudanar da aiki da kasafin kudin yadda ya kamata.

  16. Sudan da Amurka za su tura jakadu kasashen juna

    Amurka da Sudan za su tura jakadu kasashen juna a karon farko cikin shekaru sama da ashirin.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo da Firayim Ministan Sudan, Abdallah Hamdok suka sanar da haka lokacin da Mista Hamdock ya kai ziyara Washington.

    Rabon da kasashen su aika da jakadu kasashen juna tun shekaru 23 da suka gabata.

    Amurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Khartoum a 1996, a cewarta saboda ta'addanci.

    Amurka ta sake bude ofishin a 2002 ba tare da jagorancin wani jakada ba, sai mai kula da ofishin kawai.

  17. 'Yan ci rani 57 sun mutu a gabar tekun Mauritaniya

    A kalla mutum 57 suka mutu a yayin da jirgin ruwansu ya kife a gabar tekun Mauritania, a cewar hukumar kula da da 'yan ci rani ta Majalisar Dinkin Duniya.

    A makon da ya gabata ne jirgin ruwan ya bar Gambiya dauke da 'yan ci rani 150, a cewar Kungiyar da ke kula da Kaura ta kasa da kasa.

    Wadanda suka tsira sun shaida wa MDD cewa mai ne ya kare wa jirgin a yayin da yake tunkarar Gabar tekun Mauritaniya.

    A baya wannan hanyar ce 'yan ci rani daga yankin Afirka Ta Yamma ke bi a kokarinsu na tafiya Turai, amma yanzu sun fi bin hanyar Libiya.

    Gabar Teku

    Asalin hoton, AFP

  18. An kama jarka 23 ta man fetur boye a cikin makara

    Jarkokin man fetur

    Asalin hoton, NAN

    Bayanan hoto, Gwamnatin Najeriya na yaki da fasa kwaurin kayayyaki ba man fetur kadai ba

    Kwamiti mai yaki da fasa kwaurin man fetur a Najeriya na hukumar Customs ya kama wasu jarkoki makare da man fetur boye a cikin makara a kan iyakar Ikorodu ta jihar Legas.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa jarka 23 aka boye a cikin makara guda biyu, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya bayyana.

    Abdullahi Maiwada ya kara da cewa an dauko makarar ne a mota kirar Mazda 626 mai lambar LSD 617 CW.

    "A yunkurinmu na ci gaba da yaki da fasa kwauri, kwamitin hadin gwiwa mai yaki da fasa kwaurin man fetur na shiyyar Ogun I sun kama jarka 13 mai cin lita 25 da kuma jarka shida mai cin lita 10 ta man fetur boye a cikin makara guda biyu," in ji shi.

  19. Majalisar jihar Kano ta amince da dokar kirkiro sabbin masarutu

    Umar Abdullahi ganduje

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin jihar Kano ta sa hannu kan dokar nan mai cike da ce-ce-ku-ce ta kirkiro sabbin masarautu a jihar, wadda ta bukaci a kirkiro karin masarautu hudu a jihar.

    An sa hannu kan dokar ne a yau Alhamis bayan da majalisar zartarwar jihar ta aikawa majalisar dokokin da ita ranar Litinin.

  20. Kotu ta ce a mayar da El-Zakzaky da matarsa gidan yari

    Wata kotu da ke zama a Kaduna ta yanke hukuncin mayar da jagoran kungiyar IMN a Najeriya Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa gidan yari daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya.

    Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.

    Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam'ian tsaro a Zariya.

    Alkalin Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga ci gaba da sauraron shari'ar har zuwa 9 ga watan Fabrairun 2020.

    A watan Maris ne Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga sauraren karar har sai baba ta gani sakamakon sanya shi cikin mambobin kotun sauraron kararrakin zabe.

    zakzaky

    Asalin hoton, Getty Images