Mai kudin duniya zai yi takara da Donald Trump

Asalin hoton, AFP
Mai kudin duniya na 14, Michael Bloomberg yana sake sansana kujerar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrats.
Attajirin wanda tsohon magajin garin birnin New York ne ya ce yana da shakku wajen mutanen da suke son fitowa takara domin ba za su iya kayar da Donald Trump ba a zaben 2020.
Ana sa ran dan kasuwar mai shekara 77 zai gabatar da tsare-tsarensa a ranar Juma'ar nan domin neman cin zaben cikin gida da za a yi a Alabama.
To sai dai shugaba Trump ya yi wa Michael Bloomberg ba'a, inda ya ce " Idan akwai mutumin da nake son takara da shi shi ne Michael wanda karamin alhaki ne."
Mutum 17 ne dai ke takarar kujerar shugabancin a jam'iyyar Democrat.
Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, da Senator Elizabeth Warren da Senator Bernie Sanders su ne a gaba-gaba.

Asalin hoton, Chip Somodevilla/Getty Images







