Ana karancin takardun kudi a Liberia

Asalin hoton, Getty Images
Al'umar kasar Laberiya sun dasa dogon layi a injinan cirar kudi a bankuna sakamakon karancin takardun kudi da ake fama da shi.
Su ma wadanda ke cikin bankuna sun koka kan yadda ba a samun dalar kudin kasar kamar yadda aka saba.
Ma'aikatar kudin Laberiya ta sanar da cewa bankunan kasuwanci na fama da karancin kudi, saboda mutane sun jibge su a gida ba tare da kai su asusun ajiyarsu ba.
Amma masu sharhi na ganin hakan ya faru ne sakamakon rashin yarda tsakanin abokan hulda da bankunan kasar.
Ba wannan ne karon farko da kasar ke fuskantar matsala irin haka ba. Ko a shekarar 2018 an samu matsalar batan dabon sabbin miliyoyin dalolin da aka buga daga inda aka dauko su zuwa babban bankin kasar.
Duk da cewa ba a bayar da rahoto kan wannan ba, to amma bincike ya nuna an buga sama da dala miliyan 10 na kudin Laberiya ba tare da amincewar gwamnati ba.
Tattalin arzikin kasar na fuskantar koma baya, yayin da kayan amfanin yau da kullum suka yi tashin gwauron zabbi, hakan ya shafe kayayyakin da ake shigo da su kasar.
Ko a farkon shekarar nan sai da akai ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, domin kiran gwamnati ta dauki matakin sassauta wa 'yan Laberiya.











