Matsananciyar yunwa ta kashe giwaye 55 a Zimbabwe

Asalin hoton, Getty Images
A kalla giwaye 55 ne suka mutu a Zimbabwe cikin watanni biyu a gidan ajiye namun daji na Hwange da ke kasar.
An bayyana cewa yunwa ce ta haddasa mutuwar giwayen.
Mai magana da yawun gidan ajiye namun dajin wato Tinashe Farawo, ya ce ''giwayen sun mutu ne sakamakon yunwa kuma wannan babbar matsala ce.''
Fari a Zimbabwe ya sa shuke-shuke sun mutu a kasar.
An bayyana cewa da dama cikin 'yan kasar na bukatar taimakon abinci.
Ko a watan Agusta sai da Shirin Samar da Abinci na Duniya ya bayar da rahoto kan cewa mutum miliyan biyu na cikin barazanar fadawa cikin wani hali irin na yunwa a kasar.
An ce an ga wasu daga cikin giwayen sun mutu kusan mita 50 daga wani kududdufi - wannan na nufin sun yi tafiya mai nisa sun mutu kafin su isa wurin ruwan.
Mista Farawo ya bayyana cewa giwayen sun cinye tsirrai da dama a Hwange. A da, gidan namun daji na Hwange na daukar giwaye kusan dubu 15 amma a yanzu akwai giwaye kusan dubu 50.
Ya bayyana cewa hukumar da ke sa ido da lura da namun daji a kasar ba ta samun tallafi daga gwamnatin kasar kuma hukumar ta yi ta kokarin gina rijiyoyi amma ba ta da kudin da za ta ci gaba da yin hakan.











