An kama mutumin da ya kulle 'ya'yansa gida tsawon shekaru 9

Asalin hoton, EPA
An kama wani mutumi mai shekaru 67, da ke zama a wani wuri na sirri a wani gidan gona da ke Netherlands.
Kamun nasa ya zo yan sa'o'i bayan an kama wani mutun dan kasar Austria ya ari gidan.
Yara shida ne su ka shafe shekaru tara a boye a gidan gonar da ke kusa da wani kauye da ake kira Ruinerwold.
Rahotanni sun ce mutanen da aka kama anyi amanna cewa sun tsare yaran ne ba bisa yardar su ba.
Yan sanda sun ce daga cikin wadanda aka tsaren akwai matasa shida da suka hada da mata hudu da maza biyu, kuma mahaifin nasu na fama da cutar shanyewar jiki.
Yadda lamarin ya faru
An tona asirin mutanen ne a lokacin da babban dan mutumin mai suna Jan, ya tafi wata mashaya a garin na Ruinerwold.
Daga nan ne mai mashayar ya sanar da yan sanda cewa yaron ya fadamasa cewa bai taba zuwa makaranta ba kuma ya gudo ne yana neman taimako.

Asalin hoton, Reuters
Daga nan ne 'yan sanda suka je gonar, inda suka sami 'yan uwan Jan da mahaifinsa da kuma wani mutum mai shekaru 58. Mutumin dan kasar Austria ya gurfana a gaban kotu, inda aka tsare shi na tsawon kwanaki 14 da zargin hannu a tauye wa yara hakki da kuma fitar da kudade ba bisa ka'ida ba.
Yan sandan sun kara da cewa yaran sun shaida mutumin da ake kira Gerrit Jan van D, to amma ana kan binciken cikakkiyar alakarsu da shi.
An gano makudan kudade a cikin gonar.
A cewar sanarwar, 'yan sanda za su gudanar da bincike don gano yiwuwar sauya musu tunani.
Wata kafar sadarwar Netherlands ta ruwaito cewa mahaifin yaran da mutumin da aka samu a tare da su tsohon abokin shi ne kuma sun hadu ne a wata coci da da ke da asali a Koriya ta Kudu.
Wani mai magana da yawun cocin ya bayyana cewa rabon su da ganin Mr Gerrit tun a shekarar 1987, kuma tun a lokacin ya raba gari da mahaifansa.
Hakama ya ce yana tunanin Mista Gerrit na kokarin kebewa ne don kafa cocinsa kamar yadda wasu jama'a ke da irin wannan akida.
Wani dan uwansa ya ce tun a lokacin yana da wasu akidu da ba sa son suyi magana a kansu.

Asalin hoton, Facebook/Jan van D
Wasu daga cikin mutanen garinsu sun zaci ya shiga harkar cocin 'Moonies' kuma tuni ya mutu a Koriya ta Kudu.
To amma ana tunanin ya auro mahaifiyar yaran ne daga Jamus kuma ta mutu a shekarar 2004, inda shi kuma ya kwashe su zuwa Netherlands.
Mataimakin sifetan 'yan sanda da ke arewacin Netherlands ya tabbatar da tsare yaran a gidan gona tare da hana su zuwa ko'ina.











