Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 28 a Ghana

Asalin hoton, My JoyOnline
A kalla mutum 28 suka mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan kwashe kwana takwas ana mamakon ruwan sama a arewa maso gabashin Ghana.
Hukumomi na fargabar cewa yawan mutanen da suka rasu zai karu, kuma gidaje 1,264 ne wani bangarensu ya lalace yayin da guda 286 suka lalace gaba daya.
Hukumar kula da hadurra ta kasar ta fara aikawa da kayan agaji ga mutane 600 da ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu.
"Rahoton da aka yi kan lamarin na baya-bayan nan ya nuna cewa mutum 28 sun mutu a yankin Upper East da Ghana. Har yanzu kuma ruwan ake yi. Mutum 640 ne aka raba da muhallansu," in ji kakakin hukumar George Ayisi, ranar Laraba.
An ajiye mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu a coci-coci da makarantu.
Ma'aikatar hasashen yanayi ta Ghanar ta yi hasashen cewa za a samu karuwar ruwan sama a fadin kasar a makonni masu zuwa, kuma ta yi hasashen cewa za a iya samun ambaliyar ruwa.
Kungiyoyin agaji sun bukaci a kara kai agaji ga yankunan da abin ya shafa.







