Najeriya: Za a daure malamai masu lalata dalibai
Majalisar Dattawan Najeriya ta gabatar da kudurin dokar kare dalibai mata na jami'o'i daga cin zarafin.
Kudurin dokar na zuwa ne bayan rahoton binciken kwakwaf da BBC ta yi, inda ta bankado yadda wasu malaman jami'a a Najeriya da Ghana ke lalata da dalibai mata.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda shi ne ya gabatar ta kudurin ya bayyana fatan cewa rahoton na BBC zai taimaka wa kudurin dokar samun goyoyn baya.
Sanata Omo-Agege ya bayyana cewa ba zai lamunci cin zarafi ko nenam yin lalata da dalibai a jami'o'i ba.
Idan 'yan majalisar suka amince kudurin ya zama doka, zai haramta wa malaman jami'a yin kowane nau'in neman yin lalata da dalibansu.
A karkashin dokar wacce aka gabatar wa zauren majalisar a ranar Laraba, an tanadi daurin da ya kai na shekara 14 ga duk malamin da aka kama da laifin yin mu'amalar jinsi da wata daliba.
A 2016 ne aka fara gabatar da kudurin dokar amma majalisun kasar suka ki amincewa da shi.
Wasu na adawa da dokar saboda bata kunshi cin zarafi ko neman yin lalata a wuraren aiki ba, duk da cewa ta yi maganar kariya idan aka samu amincewar wanda abin ya faru da su.
Yanzu sabuwar dokar ta cire batun kare wadanda suka aikata laifin da amincewar wadanda abin ya shafa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
BBC ta fara yada bidiyon binciken yadda malaman jami'a ke yin lalata da dalibai mata a Jami'ar Legas da Jami'ar Ghana, a cikin wani rahoto na tsawon minti biyar mai suna Binciken BBC: Yadda malaman jami'a ke lalata da 'yan mata, a ranar Litinin.
Abin da binciken na BBC ya fallasa na yadda malaman ke yin fasikanci da dalibai mata ya fusata mutane, kuma ya yi sanadiyyar dakatar da malamai hudu da hotunansu suka bayyana a binciken na musamman.
Malaman sun musanta aikata laifin da ake zarginsu.
Abin da bidiyon ya nuna
Ma'aikatan BBC sun dauki bidiyon wasu malaman jami'a hudu a asirce, inda malaman ke aikatawa ko neman yin masha'a da dalibai mata.
Bidiyon ya nuna Dokta Boniface Igbeneghu, malami a Jami'ar Legas kuma limamin coci a lokacin da yake yin batsa da tayin aikata fasikanci da wakiliyar BBC da ta badda kama a matsayin dalibai mai shekara 17 da ke neman gurbin karatu a jami'ar.
Daga baya Dokta Boniface ya tattaba ta kuma ya nemi ta sumbace shi a cikin ofishinsa da ke kulle.
An kuma ga hotonshi yana mata barazanar cewa zai fada wa mahaifiyarta cewa "ba ta yi masa biyayya" ba.
Mutanen biyu da suka hada da Farfesa Ransford Gyampo da Dokta Paul Kwame Butakor, an dakatar da su daga aiki.
Sai dai sun musanta zargin da ake masu a rahoton cewa suna yin lalata da dalibai domin su ba su maki mai kyau.











