#SexForGrades: Coci ta dakatar da malamin jami'a kan binciken BBC

Asalin hoton, TWITTER/@kikimordi
Cocin The Foursquare Gospel Church a Nigeria ta ce ta raba gari da Dakta Boniface Igbeneghu, wanda yana daya daga cikin malaman jami'ar da aka nuna a bidiyon binciken BBC yana kalaman lalata ga 'yar jarida, wadda ta yi badda-kama a matsayin daliba.
Dakta Boniface fasto ne a cocin, kuma cocin ta sanar a shafinta na Twitter cewa: "Shugabancin wannan coci ya samu labarin abin da aka nuna Dakta Boniface yana aikatawa a bidiyon binciken BBC Africa Eye.
"Mun nesanta kanmu baki daya daga abin da ya aikata sannan kuma mun yi alkawarin daukar matakin da ya dace.
"Kazalika mun bukaci faston da ya ajiye duk wani mukami da yake rike da shi a wannan coci mai albarka."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da dabi'ar malaman da aka nuna a rahoton.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Ya rubuta cewa:"Yanzun nan na karanta labari game da #SexForGrades (lalata da malaman jami'o'i ke yi da mata domin ba su maki) a jami'o'in Yammacin Afirka. Ba za ta sabu ba, wajibi ne al'ummarmu ta dakile wannan dabi'ar."
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce dole ne a nemi hanyoyin hukunta malamai masu irin wannan halin.
#SexForGrades
Maudu'in #SexForGrades shi ne abin da yake tashe a shafukan sada zumunta tun daga farar safiyar yau Litinin a shafukan sada zumunta a kasashen Ghana da Najeriya, inda a kasashen ne jami'o'in da aka yi binciken suke.
Masu amfani da shafukan na kira ga BBC da ta yi kokarin bankado malaman jami'a a wasu jami'o'in nahiyar Afirka.
Da yawa suna kira da a kama malaman jami'ar da aka nada suna cin zarafin dalibai mata a cikin rahoton na BBC.
Rahoton na minti 13 mai taken #SexForGrades na sashen binciken kwa-kwaf na BBC Africa Eye, ya bayyana yadda Dakta Boniface Igbeneghu na Jami'ar Legas da Farfesa Ransford Gyampo na Jami'ar Ghana ke amfani da mukaminsu wajen bai wa dalibai mata maki a madain tarawa da su.
Wasu rahotanni daga Ghana na cewa an yi wa Farfesa Ransford ihu a yau bayan ya shiga aji domin yi wa lacca.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Omo Grandma @oluwaseyii01 ya ce "BBC don Allah ku zo jami'ar Ilorin."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
Shi kuwa fitaccen marubucin nan Elnathan John cewa ya yi ai idan ba ka taba cin karo da maganar fyade ko cin zarafi ba yayin da kake jami'a to kai ne ba ka so ka ji ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 6
Obrien Obahi @obrienthagreat ya ce: "Hatta masallatai da coci-coci suna sane da wannan aika-aikar, BBC ya kamata ku ziyarci Jami'ar Benini (UNIBEN), za ku samu kayatattun bidiyo."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 7