Wani mai kwarmata bayanai na biyu kan Donald Trump ya bayyana

US President Donald Trump returning to the White House after a game of golf on October 5 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaba Trump na Amurka a yayin da ya koma Fadar White House daga wasan golf ranar Asabar

Wani mutum na daban ya bayyana a binciken da ake yi kan rawar da Shugaban Amurka Donald Trump ya taka kan badakkalar Ukraine.

Lauyoyin mutum na farko da ya kwarmata bayanan sirri kan Mista Trump ne suka sanar da wannan ci gaban.

Mark Zaid ya sanar da tashar talabijin ta ABC News cewa mutumin na biyu shi ma jami'i mai tattara bayanan sirri ne na gwamnatin Amurka, kuma tuni ya gana da jami;in da ke jagorantar binciken.

Mista Trump ya soki jagororin jam'iyyar Democrat a cikin daren Lahadi, inda ya bayar da shawarar su ma a tsige su.

Kawo yanzu babu wani cikakken bayani game da ko waye mutumin na biyu da bayanan da ya kwarmata kan Mista Trump.

Amma Mista Zaid ya ce mutumin na da muhimman bayanai game da zarge-zargen da ake wa Mista Trump na wata hira da yayi ta wayar tarho da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ranar 25 ga watan Yuli.

Wannan binciken da ka iya kai ga tsige Mista Trump ya samo asali ne daga wannan tattaunawa da yayi da Shugaban na Ukraine.