Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 100 a Indiya

Asalin hoton, BBC Hindi
Sama da mutum 100 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihohin kasar Indiya na Uttar Pradesh da kuma Bihar, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar.
Wasu hotunan da ke nuna yadda ruwa ya mamaye titunan birane da kuma yadda ya yi tasiri kan rayuwar mutane na fitowa daga yankunan.
Titunan jiragen kasa da hanyoyin mota da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu har ma da wutan lantarki baki daya sun shiga wani hali a jihohin biyu.
Wani rahoton gwamnatin Uttar Pradesh ya ce mutum 93 ne suka mutu tun a ranar Alhamis.
A yankin gabashin Uttar Pradesh ambaliyar ta sa jami'ai sun sauya wa fursunoni 500 daga gidan yarin Ballia zuwa wasu wuraren daban bayan ruwa ya shiga cikin ginin.
Kotun majistre ta Additional District ta bayyana cewa tana jiran amincewar hukumomi domin su mayar da dukkanin fursunoni 850 zuwa Azamgarh - nisan kusan kilomita 120 kenan.
Mutum 29 ne suka mutu a jihar Bihar, in ji jami'an kula da annoba a yankin. Barnar da ambaliyar ta haifar a babban birnin yankin ta jawo cecekuce.
Kazalika wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta na wani mutum da yake kokarin fitar da babur dinsa mai kafa uku daga cikin ruwan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X


Asalin hoton, BBC Hindi
Mataimakin gwamnan yankin, Sushil Modi, shi ma an tserar da shi daga gidansa a ranar Litinin, kamar yadda rahoton ANI ya tabbatar.
Jami'an kula da annoba ne suka fitar da shi da iyalinsa daga gidan nasa, wanda ruwa ya mamye.

Asalin hoton, BBC Hindi
Kazalika irin wadannan rahotannin ake samu daga makwabciyar jihar wato Uttar Pradesh.


Asalin hoton, BBC Hindi

Asalin hoton, BBC Hindi
Gwamnatin yankin ta nemi agajin rundunar sojojin saman Indiya na taimakon jirage masu saukar ungulu da kuma injina domin janye ruwan.











