Khashoggi: Yadda aka gano wanda ya kashe shi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Jane Corbin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Panorama
Gargadi: Akwai abubuwa marasa dadi

Na bi ta wani layi mai bishiyoyi jere a wata unguwa da ke Istanbul domin zuwa wani katafaren gida mai launin ruwan madara wanda aka sanya wa kyamarorin daukar zirga-zirgar mutane wato CCTV.
A shekarar da ta gabata wani dan jarida dan asalin Saudiyya mai gudun hijira a Turkiyya ya kai irin wannan ziyara a ofishin. Kyamarar CCTV ta dauki hotonsa amma daga nan ba a sake ganin hoton nasa ba.
Jamal Kashoggi ya shiga ofishin jakadancin Saudiya inda wasu 'yan ina-da-kisa sun kashe shi.


Asalin hoton, Reuters

Amma hukumar tara bayanan sirri ta Turkiyya ta dauki sautin yadda aka tsara da aiwatar da kisan Khashoggi a sirrance. Mutane kalilan ne suka ji faifen sautin. Biyu daga cikinsu sun yi wa shirin BBC mai suna Panorma bayani na musamman.
Barista Baroness Helena Kennedy 'yar kasar Birtaniya ta saurari jawabin da Jamal Khashoggi ya yi kafin mutuwarsa.
"Irin abin firgici da tashin hankalin da ke cikin muryar mamacin, wanda aka dauka kai tsaye, zai sa gaba daya mutum ya kidime."



Kennedy ta yi cikakken bayani a kan yadda ta ji tattaunawa tsakanin 'yan ina-da-kisan kasar Saudiyya.
"Za ka iya jin su suna dariya. Hankalinsu kwance. Suna jira tare da yakinin cewa mutumin zai zo kuma za a kashe shi a yi masa gunduwa-gunduwa."
Kennedy na daga cikin 'yan tawagar da babbar wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan kisa ba bisa ka'ida ba, Agnès Callamard ke jagoranta.
Callamard kwararriya a kan kare hakkin bil'adama ta tabbatar mini cewa za ta yi amfani da ofishinta wajen bincikar kisan Khashoggi, sakamakon jan kafar da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na kaddamar da bincike a kai.



Sai da ta dauki mako daya tana lallashin hukumomin tara bayanan sirri na Turkiyya su ba ta dama ta saurari faifen sautin tare da Kennedy da mai yi musu fassarar larabci.
"Manufarmu ta samun izinin hukumar shi ne domin mu samu damar tsarawa da tabbatar da cewa an tsara kisan ne, kuma mu ga an biya diyya," inji ta.
Masu binciken sun samu damar sauraron sautin minti 45 da aka tattaro daga wasu rana biyu masu matukar muhimmanci.

Jamal Khashoggi ya yi makonni a Istanbul kafin a kashe shi. Birnin Istanbul na daga cikin wuraren da suka zama mafaka ga galibin masu adawa da gwamnatoci a yankin gabas ta tsakiya.
Lamarin ya faru ne 'yan kwanakin kadan bayan an yi wa Khashoggi, mai shekara 59 kuma mahaifin 'ya'ya hudu baiko da wata kwararriyar mai bincike, Hatice Cengiz.
Yayin da Khashoggi da Hatice ke shirin fara rayuwa a matsayin iyali a birnin Istanbul, angon na bukatar gabatar da takardun shedar rabuwarsa da matarsa ta farko kafin ya kara aure.
A ranar 28 ga watan Satumba, Kashoggi da Cengiz sun ziyarci ofishin birnin Istanbul inda aka sanar da su cewa sai sun kawo takardun rabuwar aurensa daga ofishin jakadancin Saudiyya.
"Babu makawa sai ya je ya samo takardun daga ofishin jakadancin Saudiyya kafin a daura mana aure a hukumance saboda ba zai iya komawa kasarsa ba," kamar yadda ta shaida mini a wata rumfar shan shayi.



A farko Khashoggi ba dan adawar tsarin gwamnatin kasarsa ba ne. Na fara haduwa da shi ne shekara 15 da suka gabata a ofishin jakadnacin Saudiyya a Landan. A lokacin yana aiki a ofishin ne a matsayin kakakin jakadan Saudiyya.
A lokacin na yi hira da shi a kan wani harin kungiyar Al-qaeda. Kashoggi ya san shugaban kungiyar, Osama bin Laden wanda dan Saudiyya na gomman shekaru. Da farko yana goyon bayan manufofin Al-qaeda na kawar da gwamnatoci masu kama-karya a yankin gabas ta tsakiya.
Amma daga baya ya fito ya kalubalanci aika-aikar da kungiyar ke tafkawa bayan da ya kara zama mai sassaucin ra'ayi kuma magoyin bayan tsarin dimokuradiyya.



A 2007, Kashoggi ya koma Saudiyya a matsayin editan jaridar Al-watan mai goyon bayan gwamnati. Amma bayan shekara uku aka sallame shi saboda abin da aka kira "neman kawo mahawara tsakanin al'ummar kasar".
Bayan guguwar neman sauyin da ta taso a kasashen Larabawa a 2011, Khashoggi ya yi ta kalubalantar abin da ya kira danniya da mulkin kama-karya na gwamnatin Saudiyya.
A 2017 aka haramta masa yin rubuce-rubuce, inda daga nan ya tsallaka zuwa Amurka domin kashin kansa domin neman mafaka. An kuma tilasta wa iyalinsa rabuwa da shi.
A zamansa na Amurka, Kashoggi ya zama marubuci a jaridar Washington Post, inda ya rubuta wasu makala 20 masu zafi shekara daya kafin rasuwarsa.
"Ya kan saba ka'ida a lokacin da yake edita a Saudiyya," inji abokinsa David Ignatius, dan jarida mai binciken kwakwaf kuma babban marubuci kan harkokin waje a Washington Post.
"Abin da na sani game da Jamal shi ne bayyana ra'ayinsa kan jefa kansa cikin hadari."



Yawancin sukar da Khashoggi ke yi yana yin su ne ga yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman.
Mutane da dama a yammancin duniya na yabon yarima Muhammad bin Salman wanda suke gani a matsayin mai kawo sauyi da tafiya daidai da zamani da hangen nesa a kasarsa.
A gida Saudiyya kuma, yarima MBS kamar yadda ake kiransa a yammacin duniya, na kokarin murkushe 'yan tayar da kayar baya, wanda Kashoggi ke yawan sukan hakan a Washington Post.


Asalin hoton, Reuters

Hakan ba abin da yariman ke neman duniya ta sani ba ne game da kasar.
"Ina jin hakan ne ya fusata yariman, har ya rika umurtar hadimansa da su yi maganin matsalar," inji Ignatius, marubucin harkokin siyasa kuma mai yawan ziyartar Saudiyya.
A Istanbul kuma jami'an Saudiyya sun samu damar "yin wani abu" game da Khashoggi.

Ranar da ya fara ziyartar ofishin jakadancin, ba a yarda Cengiz ta shiga ba.
Ta gaya mana cewa Khashoggi ya fito daga ginin da murmushi a fuskarsa. Ya ce mata jami'an sun yi mamakin ganinsa har suka ba shi shayi.
"Ya ce ba wani abin damuwa, ya yi kewar kasarsa sosai kuma shakar iskar wurin ya sa masa nutsuwa."
Jami'a ofishin sun ce masa ya dawo bayan kwana biyu.
Tafiyarsa ke da wuya sai ofishin ya buga waya zuwa Riyadh a Saudiyya - kuma hukumar tara bayanan sirri ta Turkiyya ta nadi sautin kiran wayar.
Callamar ta ce "Abin mamaki game da kiran wayar shi ne yadda aka ambaci Khashoggi a matsayin daya daga cikin mutanen da ake nema."
Ana kyautata zaton cewa wayar da aka yi ta farko ta farkar da babban jami'in da ke gudandar da ofishin Yarima MBS mai suna Saud Al-qahtani.
A cewarta "Wani ne a ofishin sadarwan ya ba da umurnin yin aikin. Za a iya fahimtar cewa tuntubar ofishin sadarwan tamkar tuntubar Saud Al-qahtani ne."
"Sau da dama an sha ambaton Al-qahtani a yunkurin da ake yi kan wasu mutane."


Asalin hoton, Twitter

A baya an zargi Al-qahtani da hannu a tsarewa da azabtar da masu tayar da kayar baya a Saudiyya da manyan mutanen da ake zargi da rashin da'a. Cikinsu har da wata mata 'yar fafutuka da ta fara tuka mota kafin a janye takunkumin hana mata tuki a kasar.
A cikin rubuce-rubucensa, Khashoggi ya zargi Al-qahtani da 'katse alakar' yarima Muhammad bn Salman da wasu mutane.
"Qahtani ya fara gudanar da wani aiki na musamman - miyagun ayyuka a sirranci," inji Ignatius, wanda ya taba bincikar hadimin yariman. "Wannan ya zama daga cikin ayyukansa wanda ya aiwatar da karfin tuwo."
"An dauki sautin kiran waya akalla guda hudu tsakanin Riyada da ofishin jakadancin da ke Istanbul a ranar 28 ga watan Satumba. Sautin da aka dauka ya hada da na hirar da aka yi tsakanin jakadan da shugaban tsaro na ma'aiktar harkokin wajen Saudiyya, wanda ya sanar da jakadan game da wani muhimmin aiki na sirri - aiki domin kasa - da aka shirya.
Ba na kokwanton cewa an tsara abin da kyau sosai kuma da ga sama aka kitsa shi," inji Kennedy.
"Wannan ba aikin tagajan-tagajan ba ne."

A ranar 1 ga watan Oktoa wasu jami'an tara bayanan sirri uku a ofishin yarima MBS suka sauka a Istanbul.
Callamard na zargin cewa jami'an sun je Istanbul ne a lokacin domin lura da fahimtar yanayin wurin.
"Da alamu sun je ne su duba yanayin ofishin jakadancin domin su fahimci irin abin da zai yiwu da wanda ba zai yiwu ba."
Na hadu da wani tsohon kwararren jami'in kasar Turkiyya da ya shekara 27 yana aiki da hukumar tattara bayanen sirrin kasar, mai suna Metin Ersöz a Istanbul.
Metin Ersöz kwararre ne kuma a kan kasar Saudiyya da ayyukanta a musamman. Ya ce tun da Mohammed bin Salman ya zama yarima mai jiran gado, hukumar tara bayanen sirrin Saudiyya ta fara tsanantawa.



"Sun fara ne da sace mutane da kuma matsa wa masu tayar da kayar baya," inji shi.
"Khashoggi bai yi saurin fahimtar barazanar da kuma daukar matakan kariya ba, shi ya sa aka ritsa da shi."
A ranar biyu ga watan Oktoba, wani jirgin sama na alfarma ya sauka a Istanbu dauke da wasu 'yan Saudiyya su tara, ciki har da Dokta Salah Al-tubaigy, kwararre a bincike kan tasirin cuta da musabbabinsu da gwaje-gwaje a kansu.



Bayan nazarrin mutanen da bangarorin da suka fito, sai Callamard ta fara zargin ko su ne 'yan ina-da-kisan.
"Jami'an gwamnati ne suka aiwatar da aikin kuma a matsayinsu na ma'aikatan gwamnati," a cewarta.
"Biyu daga cikin mutanen na amfani da takardun fasfo na jakadanci ne."
Ersöz ya ce baiwatar da irin wanan aiki ba ya yiwuwa sai dole an samu izinin sarkin Saudiyya ko yarima mai jiran gado.
'Yan tawagar Saudiyyan sun sauka ne a wani otal mai suna Mövenpick Hotel da ke kusa da ofishin jakadancin.


Asalin hoton, Reuters

Kafin karfe 10, kyamarar CCTV ta nuna hoton daya daga cikin mutanen yana shiga ofishin jakadancin.
Bayan sauraron faifen sautin, Kennedy ta yi amannar cewar Maher Abdulaziz Mutreb shi ne ya jagoranci aikin.
Maher yakan yi tafiye-tafiye tare da yarima mai jiran gado a fakaice kuma a kusa da shi cikin dogarensa.
"A wayar da jakadan ya yi da Maher, an yi nuni da cewa 'mun samu bayani cewa Khashoggi zai zo ranar Talata'," inji Kennedy.


Asalin hoton, Getty Images

A safiyar biyu ga watan Oktoba ne aka kira Khashoggi ya je ya karbi takardunsa a ofisihin jakadancin.
A yayin da Khashoggi da Cengiz ke hanyarsu ta zuwa ofishin, Mutreb da Dr al-Tubaigy na can a ofishin suna wata tattaunawa mai ban tsoro.
"Yana magana a kan yadda yake binciken sanadin mutuwar mutane yana dariya," inji Kennedy.
"Yana cewa, 'na kan kunna waka idan ina yanka. Wani lokaci kuma da shayi ko sigari a hannuna.'"
Faifen sautin ya nuna cewa likitan ya san abun da ake so ya yi, inji Kennedy.
Ta ce ta ji likitan na cewa "Karon farko ke nan da zan sassara a kasa. Ko mahauci sai ya rataye dabba kafin ya sassara ta."
An riga an tanadi wani ofishi inda ka shimfida leda a kasa kuma an ba wa dukkan ma'aikata 'yan kasar Turkiyya hutu.
"Suna magana kan lokacin da Kashoggi zai isa wurin inda suke cewa, 'Shin dabbar layyar ta iso?' Abin da suke kiransa ke nan, a cewar Kennedy.
Haka ta rika karanto wadanan bayanai daga wani littafi cikin kaduwa.


Asalin hoton, Reuters

Da karfe 1:15 na rana CCTV ya nuna Khashoggi na shiga ofishin jakadancin.
"Ina iya tunawa bayan isar mu wunin tare, da muka isa gaban ofishin sai Jamal ya ba ni wayoyinsa ya ce, 'Masoyiyata ki jira ni a nan, sai anjima,'" inji Cengiz.
Khashoggi ya san za a karbe wayoyinsa a kofar shiga ga shi ba ya son jami'an Saudiyya su samu bayanansa na sirri.
Faifen muryar ya nuna cewa masu tarbar baki sun same shi inda suka sanar da shi cewa hukumar 'yan sanda ta duniya ta ba da izinin tsare shi kuma wajibi ne ya koma Saudiyya.
An ji shi inda ya ki yarda ya aika wa dansa rubutaccen sako da zai tabbatar wa iyalensa cewa yana cikin koshin lafiya.
Daga nan aka fara kokarin gamawa da Jamal Khashoggi.








"An kai wani matakin da ake jin Khashoggi, wanda aka sani da jarumta ke nuna alamar ya fahimci ana so a yi wani aika-aika," inji Kennedy.
"Akwai razanarwa a yadda muryarsa ke sauyawa. Za a iya jin tashin hankalkin duk ya mamaye faifen sautin."
Callamard ba ta da yakinin cewa Khashoggi ya san abin da 'yan Saudiyya suka shirya: "Ba na ganin ya yi tunanin za a iya kashe shi, amma tabbas ya yi tunanin za a iya sace shi. Ya na ce masu 'Allura za ku yi min?' kuma aka ce masa e.
Kennedy ta ce ta ji Khashoggi sau biyu yana tambayar ko sace shi aka yi, inda ya ke cewa, "Ya za a yi haka a cikin ofishin jakadanci?'"
"Karar da aka ji bayan hakan na iya nuna cewa makureshi aka yi. Watakila an yi amfani da leda an rufe kansa," inji Callamard. "An kuma rufe bakinsa da karfin tsiya - da hannu ko da wani abu."
"Za ka ji ana cewa, 'Bari ya yanka.' kuma kamar muryar Mutrebe.
"Daga nan sai aka ji wani na cewa "An gama,' wani kuma na cewa, 'Cire, cire. Sa wannan a kansa. Nade ta.' Ba komai na yi tunani ba illa sun cire kansa."

Ita kuma Cengiz, minti 30 ke nan da Khashoggi shiga ofishin jakandancin ya bar ta a waje.
"A lokacin ina ta tunanin rayuwata za ta kasance nan gaba - yadda daurin aurenmu zai kasance. Mun shirya wani dan karamin biki," inji ta.
Da misalin karfe 3 na rana kyamarar CCTV ta nuna motocin ofishin jakadancin sun isa gidan jakadan wanda layi biyu ne tsakaninsa da ofishin.


Wasu mutane uku sun shiga da akwatuna da jakkunan leda wadanda Callamard ke tunanin sassan jikinsa ne a ciki.
Daga baya wata karamar mota ta fito daga gidan kuma ba a ga gawar Khashoggi ba.
Bayanin abu mafi tayar da hankali a lokacin kisan fa - wukar tiyatar da aka daddatsa gawarsa da ita?
Kenndy ta ce bata ji irin karar da za ta iya dangantawa da wukar tiyatar ba a cikin faifen. Amma ta ce akwai gunji a kasa-kasa, wanda jami'an tara bayanan sirrin Turkiyya ke tunanin karar wukar tiyatar ce.
At karfe 3:53 an ga mutum biyu daga cikin 'yan ina da kisan suna fitowa daga ofishin jakadancin. Kuma na bi sawunsu da kyamarorin kan titi daga ofishin zuwa tsakiyar birnin Istanbul.
A cikinsu mutum daya na sanye da kayan Khashoggi amma takalmansa sun bambatan. Dayan kuma ya kare fuskarsa da hular sanyi kuma yana dauke da wata farar jakar leda.


Asalin hoton, Reuters

Mutanen sun nufi babban masallacin Blue Mosque. ko da suka sake bullowa, mutumin da ke sanye da kayan Kashoggi ya sauya kayan.
Daga nan suka tare tasi suka koma masaukinsu bayan sun jefar da jakar ledar da ake tunanin kayan Kashoggi ne a ciki a wani juji, kafi su shiga titin jirgi na karksahsin kasa sannan suka koma masaukinsu a Mövenpick Hotel.
"A tsara kisan da kyau ta yadda ba za a yi tunanin wani mugun abu ya faru da Kashoggi," inji Callamard.
Duk tsawon lokacin, Cengiz na can tana jira a wajen ofishin jakadancin.
"Na yi ta jira har bayan karfe 3:30. Da na fahimci cewa an tashi aiki a ofishin sai na ruga wurin na tambayi me yasa Jamal bai fito ba. Sai mai gadi ya ce bai fahimci abin da nake cewa ba."
Da karfe 4:41, Cengiz ta kagara, sai ta buga wa wani tsohon abokin Khashoggi, Dokta Yasin Aktay, waya. Jamal din ne ya ba ta lambar saboda idan ya shiga matsala.
Dokta Yasin Aktay dan jam'iyya mai mulki ne a kasar Turkiyya ne kuma ya san manyan mutane.
"Wata mata ta kira ni da wata bakuwar lamba muryarta cike da damuwa." Inji shi. "Ta ce, 'Saurayina Jamal Khashoggi ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya kuma bai fito ba.'"



Nan take Yasin ya buga wa shugaban hukumar tara bayanan sirrin Turkiyya waya kuma ya sanar da ofishin shugaba Tayyip Erdogan.
Karfe 6:30, jirgin 'yan ina-da-kisan ya riga ya kama hanyar komawa Riyadh, kasa da sa'o'i 24 da zuwansu Turkiyya.
Washegari gwamnatocin Saudiyya da Turkiyya suka fito da sanarwa masu karo da juna game da abin da ya faru a ofishin jakadancin. Saudiyya ta dage cewa Khashoggi ya bar ofishin, su kuma hukumomin Turkiyya na cewa yana ciki.
A lokacin jami'an tara bayanan sirri na Turkiyya sun riga sun fara bin diddigin hotunan kyamarorin CCTV dake ofishin da kuma kiray-kireayen waya da aka yi kwanaki hudu kafin bacewar Khashoggi.


Asalin hoton, Getty Images

Shin a lokacin sun san cewa rayuwarsa na cikin hadari, kuma idan sun sani me ya sa ba su yi masa kashedi ba?
"Ba na tunanin sun sani. Babu wata hujja mai nuna cewa suna sauraren abubuwan da ke faruwa kai tsaye," a cewar Callamard.
"Irin wannan aikin sirri ana yin sa ne a kai a kai, faruwar wani abu ne ya sa aka waiwayi faifen da aka dauka. Bacewa da mutuwar Khashoggi ce ta sa aka dauko kasakasen da aka dauka.
Ersöz ya ce tsoffin abokan aikinsa sun yi bitar kasakasen cikin nutuwa inda suka yi nazarin hotunan da aka dauka na tsawon sa'o'i 4,000 zuwa 5,000 domin gano muhimman ranaku da kuma mintuna 45 da aka gabatar wa Callamard da Kennedy.
Kwanaki hudu bayan kashe Khashoggi, sai wata tawaga ta zo daga Saudiyya da sunan ta zo ta binciki abun da ya faru.
Callamard na zargin cewa tawagar ta je Turkiyya ne domin ta batar da sawun abun da ya faru.
A karkashin dokar kasa da kasa, ofishin jakadancin na karkashin ikon Saudiyya. Sai da aka dauki makonni biyu larabawan ba su bari jami'an Turkiyya masu bincike sun shiga ba.
"Ko da jami'an Turkiya suka samu izinin shiga ofishin, ba abin da suka iya samu. Hatta kwayar halittar DNA da zata nuna cewa Khashoggi ya je wurin basu samu ba," inji Callamard.
"Abin da hankali zai gano shi ne an tsaftace wurin sosai."


Asalin hoton, Getty Images

A yammacin ranar hukumomin Turkiyya suka sanar da 'yan jarida cewa a ofishin jakadancin Saudiyya aka kashe Khashoggi.
"Jamal bai cancanci irin haka ba. Ya fi karfin a yi masa haka. Irin kisar da suka yi masa ya kashe fatana gaba daya," Inji Cengiz.
"Kisan da aka yi a cikin ofishin jakadanci a Istanbul a cikin kariyar diflomasiyya ya jefa Turkiyya cikin tsaka mai wuya.
Turkiyya ta dauki makonni hudu tana yin matsin lamba amma hukumomin Saudiyya suka musa cewa an yi kisan. Da farko sun ce fada aka yi a ofishin jakadancin. Daga baya kuma suka ce ba da izininsu aka yi kisan ba.


Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Dabarar da hukumomin Turkiyya suka yi shi ne bayyana wa 'yan jarida wasu abubuwan da suka faru. Daga nan suka gayyaci wakilai daga CIA da wasu hukumomin tara bayana sirri masu rauni, ciki har da M16 su saurari faifen sautin domin su tabbatar da cewa jami'an gwamnatin Saudiyya ne suka kashe Khashoggi.
CIA sun yi ittifakin cewa akwai kwararan hujjojin masu tabbatar da cewa Mohammed bin Salman ne ya ba da umurnin kisan. Sun kuma yi wa majalisar kasar gamsasshen bayani kan sahihancin sakamakon binciken.
Daga karshe a wajtan Janairu gwamnatin Saudiyya ta gurfanar da mutum 11 a kotu bisa zargin kashe Khashoggi, cikinsu har da Mutreb da Dokta Al-tubaigy.
Amma shi babban wanda ake zargin wato Saud al-Qahtani, ba a gurfanar da shi a kotu ba kuma ba'a gayyace shi ya ba da shaida ba.
Na samu labarin cewa an kebe shi daga mutane, har da iyalensa, amma kuma yana cigaba da ganawa da yarima Muhammad bn Salman.

Rahoton binciken da Callamard yi wa Majalisar Dinkin Duniya ya riga ya cimma matsaya.
"Babu wani yadda za a iya kwatanta abin da ya faru a karkashin dokar kasa da kasa sai dai a ce gwamnati na da hannu a kisan," a cewarsa.
A cewar Kennedy wajibi ne a dauki mataki a kan abin da ya bayyana a faifen kisan Kashoggi.
"An aikata cin amana da abin firgitarwa a ofishin jakadancin. Akwai alhaki a kan ksashen duniya na su tabbatar da ganin an gudanar da cikakken bincike", inji ta.
Turkiyya ta bukaci a kawo mata wadanda ake tuhuma domin su fuskanci hukunci a Istanbul amma kasar Saudiyyya ta ki yarda da hakan.
Gwamantin saudiyya ta ki yarda ta zanta da shirin Panorama, amma sun yi tir da "kisan gillan" tana mai tabbatar da shirinta na tabbbatar da ganin an hukunta masu laifin.
Sai dai kuma ta nesanta yarima Muhammad bin Salman daga zargin na abin da ta kira aika mummunan laifi.


Asalin hoton, Reuters

Bayan shekara guda, har yanzu ina ganin irin wahalar da matar da aka bari a bayan an katse rayuwar mijin da za ta aura ta mummunar hanya.
Da take ban kwana da ni, Hatice Cengiz ta yi mani wasiyya kan ainihin muhimmancin kisan Jamal Khashoggi.
"Ba abun takaici ba ne kawai gareni ni kadai - abin takaici ne ga dukkan mutane da sauran jama'a masu tunani irin ta Jamal da kuma masu fahimta irin tasa.


Asalin hoton, Getty Images












