Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Duniya ta fara shaida illar harin da aka kai wa Saudiyya
Farashin mai samfurin Brent ya yi tashin da bai taba yin irin sa ba cikin tun lokacin yakin tekun Fasha na 1991, bayan wasu hare-hare biyu da aka kai wa wurin hakar man kasar Saudiyya.
Hakan ya sa an samu raguwar kashi 5 cikin dari a albarkatun mai da ake samarwa a duniya.
Gangar danyen mai ta Brent ta tashi da kashi 10 cikin 100 inda ta kai Dala 66.28 kan kowace ganga.
Duk da dai an samu sauki kadan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umurnin fito da mai daga ma'ajiyar man kasar ta Amurka.
Za a kwashe makonni masu yawa kafin matatar man ta Saudiyya da harin ya shafa ta dawo aiki yadda ta saba.
Kamfanin tace mai na kasar Saudi Aramco ya ce harin ya sanya man da kasar ke samarwa ya yi kasa da ganga miliyan 5.7 a kowace rana.
Harin wanda aka kai da jirgi maras matuki ya hada har da wanda ya fada kan matatar mai mafi girma a duniya da ke kasar ta Saudiyya.
Amurka dai ta zargi Iran da hannu a harin.
Saudiyya kuma ta ce tana kokarin kashe wutar, to amma da alama kokarin nata bai isa ba - in ji Abishek Kumar, wani jami'i a Interfax Energy.
Ya kara da cewa da alama barnar da aka yi wa cibiyoyin sarrafa man fetur din na Abqaiq da Khurais na da muni.
Iran ta zargi Amurka da kokarin yaudara, bayan da sakataren wajen Amurka din Mike Pompeo ya ce Iran ce ke da alhakin kai harin.
Mr Pompeo dai ya yi watsi da ikirarin da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka yi cewa su ne ke da alhakin kai harin.