Yadda 'yan Saudiyya ke kashe miliyoyi yayin zuwa Birtaniya

'Yan Saudiyya da ke ziyartar Birtaniya sun kashe kusan rabin biliyan na kudin kasarsu, wato riyal miliyan 445 cikin wata uku kacal, inda aka yi kiyasin cewa kowane mutum daya ya kashe riyal 21,000.

Wannan bayani na dauke ne cikin wasu sabbin bayanan alkaluma da wani shafin intanet na Hukumar Yawon Bude Ido ta Birtaniya VisitBritain, ya fitar, kamar yadda kafar yada labaran intanet ta Saudi Gazette ta ce.

Jaridar Al-Watan ta ruwaito cewa yawan 'yan Saudiyyar da suka ziyarci Birtaniya ya kai 23,769 a watanni uku na farkon shekarar 2019, sai dai dalilan ziyarar sun bambanta, wasu kan je hutu ne ko harkokin kasuwanci ko karatu da sauran abubuwa.

Alkaluman sun nuna cewa yawan mata 'yan Saudiyya da suka ziyarci Birtaniya a wannan lokacin ya kai 7,366, sun kuma kashe fam miliyan 24.9, kwatankwacin riyal miliyan 114.

Shekarun matan na tsakanin 16 ne zuwa 65.

An kuma bayyana cewa 'yan Saudiyyar sun shafe kwanaki 352,257 a Birtaniya, inda maza suka shafe kwanaki 272,816, mata kuma suka shafe kwanaki 79,791.

Idan aka duba alkaluman aka kuma kwatanta da na daidai wannan lokacin a bara, an gano cewa yawan mata 'yan Saudiyya da suka ziyarci Birtaniya ya karu da kashi 76.6 cikin 100 a tsawon lokaci daya a baran, yayin da kudin da suka kashe kuma ya karu da kashi 62.8 cikin 100, haka kuma ranakun da suka shafe sun karu da kashi 224.9 cikin 100.

A hannu guda kuma ta bangaren maza an samu raguwa a kwanakin da suke shafewa da kuma kudin da suke kashewa.

Yawan ziyarar da suke kai wa Birtaniya ya ragu da kashi 34.7 cikin 100 zuwa 16,403 daga shekarar 2018, yayin da kudin da suke kashewa da kwanakin da suke shafewa suka ragu da kashi 20.6 da kuma kashi 56.6 cikin 100.

Alkaluman sun nuna cewa adadin kudin da mazan suka kashe ya kai riyal miliyan 331.