Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya ta bai wa mata damar yin tafiya ba muharrami
Hukumomi a kasar Saudi Arabiya sun sanar da sabuwar doka da za ta bai wa matan kasar damar yin balaguro ba tare da izini ko rakiyar muharrami ba - lamarin da ya kawo karshen haramcin da a baya kasar ta yi fice a kansa.
Ana ganin matakin wani bangare ne na sauye-sauyen da Yarima Muhammad Bin Salman ke gabatarwa a kasar, wadanda suka shafi fannonin rayuwa daban-daban.
Sabuwar dokar, wacce ta fara aiki da misalin karfe 12 na dare agogon Jiddah, ta ce a yanzu za a bar mata da shekarunsu suka haura 21 su nemi fasfo, sannan su yi tafiya zuwa kasashen ketare.
Wannan sauyi zai ba su damar yin wasu abubuwa masu alaka da baluguro kamar yadda maza ke yi.
Dokar ta kuma fadada damar da suke da ita ta neman aiki. A yanzu dukkan 'yan kasar na da damar yin aiki ba tare da nuna wani banbanci ba.
Kafin yanzu, dole mace ta nemi izinin mijinta, ko mahaifi, ko kuma wani dan uwanta namiji kafin ta karbi fasfo ko ta yi tafiya zuwa kasashen waje.
Za kuma su iya yin rajistar haihuwa da rashi, wanda a baya ba su damar yin hakan.
Wadannan sauye-sauye na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama ke kara matsawa kasar lamba kan batun hakkin mata. A don haka wasu na ganin kamar bayar da kai ne ga irin wannan matsi.
Saudi Arabiya kasa ce da ta yi fice wurin bin tafarkin addinin Musulunci sau da kafa, kuma a bar koyi ga al'ummar Musulmai da dama.
A don haka yayin da wasu musamman a kasashen yamma ke kallon irin wadannan sauye-sauye a matsayin ci gaba, wasu al'ummar Musulmai a ciki da wajen kasar, na yi musu kallon koma-baya da kuma kaucewa tafarkin da wadanda suka gina kasar suka dora ta a kai.