Dan uwan Boris Johnson ya ajiye mukamin minista saboda bambancin siyasa

Lokacin karatu: Minti 1

Jo Johnson, wanda kani ne ga Boris Johnson ya ce hankalinsa ya rabu biyu, "ko ya goyi bayan dan uwana, ko in goyi bayan kasata:

Mista Jo, wanda shi ne ministan kasuwanci kuma wakili ne na mazabar Orpington a yankin kudu maso gabashin birnin Landan, ya ce yana fuskantar matsanancin matsi a rayuwarsa da aikinsa.

Masana harkokin siyasa sun ce ajiye aikin da zai yi ba karamin tasiri zai yi a siysar yayan nasa ba.

Shi dai Jo Johnson ya kada kuri'ar Birtaniya ta yi zamanta ne a cikin Tarayyar Turai a lokacin da aka yi zabe raba gardama a 2016.

Shi kuwa yayansa Boris ya jagoranci masu cewa a fice ne.

Ajiye aikin da Mista Johnson din yayi ya biyo bayan korar wasu 'yan majalisa 21 'ya'yan jam'iyyar Conservative ne saboda sun ki goyon bayan Firai ministan kasar a majalisa.