Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya ta kashe mutum 42 a Jamhuriyar Nijar
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce mutum 42 ne suka rasa ransu sanadin ambaliyar ruwa, a yayin da gidaje da dama suka ruguje a ruwan marka-marka da ake yi bana.
A wasu wuraren ana alakanta ambaliyar da cikowar Kogin Kwara a yayin da a wasu kuma tsabar ruwan saman da ake shekawa ne kamar da bakin kwarya.
Rahotanni daga yankin da ke kusa da kogin Kwara, wato Issa, da kuma koramun da ke taimaka wa kogin da ruwa, sun sanar da cewa sama da shekara 50 da suka gabata, ba a taba samun irin yawan ruwan da aka samu ba, suka kai kololuwar gabar kogin na Kwara daga bangaren kasar ta Njiar, sai a 2012.
A bana a cikin wannan mako ruwan kogin na karuwa ne da tsawon santimita 10 duk safiya, abun da ya sa yawan ruwan ya kai tsawon santimita 638 wanda ya wuce mizani, har ya nuna cewa da akwai babbar matsala, kuma za ta iya haddasa babbar ambaliya.
Wannan dalili ya sa aka yi kira ga al'ummar da ke gabobin wannan kogi na Kwara daga bangaren na Nijar da su bar matsugunnansu.
A yankunan da ba su kusa da gabar kogin na Kwara, kamar jihar Katsinan Maradi, gundumar Aguie na daya daga cikin inda aka samu ambaliya, kamar yadda wani mazaunin garin, Yahuza Lawalli ya shaida wa BBC.
"Sakamakon ruwan saman da aka samu a bana, damunar ce ta zo da karancin ruwa da fari. Cikin garin Aguieruwan da aka samu, dan lokaci kadan ne dai aka yi shi, amma ya yi barna kwarai.
"An samu gidaje da yawa wadanda suka fadi, sannan aka samu wata mata da ta rasa ranta, inda daki ya kashe ta.
"A lissafin da muka yi gidajen da aka samu sun rushe sun fi 50. Katangu sun fadi wasu kuma dakuna ne suka fadi. Har yanzu wallahi ba wani taimakon da aka samu."
A taron manema labarai da ministan agajin gaggawa Lawan Magaji ya jagoranta, ya sanar da cewa zuwa jiya, alkaluman kididdiga sun nuna cewa iyalai 8,624 ne baki daya a kasar ta Jamhuriyar Nijar lamarin ambaliyar ya shafa.
Kuma wasu daidaikun mutane 69,371 ne ke cikin mawuyacin hali, a yayin da mutum 42 suka rasa rayukansu.
Ta bangaren kadarori a cewar ministan, gidaje 5,497 suka rushe. Dabbobi kuma 829 ne suka mutu.
A halin yanzu dai ana iya cewa daukacin dukkan jihohin kasar ta Jamhuriyar Nijar guda takwas, sun fuskanci barazanar ambaliyar ruwa.
Kuma a nan gaba ana sa ran lamarin zai iya kara kamari.
Taimakon gaggawa
Game da mutananen da matsalar ruwar ambaliyar ruwar ta shafa, cewar ministan, da kyar aka samu kashi 30 cikin 100 na kayayyakin bukatar al'ummar da ke cikin wannan mawuyacin hali, wanda gwamnati ta bayar da kuma kungiyar kula da masu kaura ta kasa da kasa da asusun yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF).
Sai dai ana samun tsaiko wajen aika taimakon ga wadannan jama'a.
Tuni gwamanti ta yi tanadin tan 2,780 na abinci a cikin jihohin kasar baki daya.
Su kuma abokan hulda masu hannu da shuni, sun rarraba kayayyakin bukata da ba na abinci ba, ga mutum 1,198 daga cikin mutum 8,624.
To sai dai kuma wata matsala da ake hange nan gaba ita ce, da dama daga cikin wadanda suka rasa gidajen nasu sanadiyyar wannan ambaliyar ruwa, na zaune ne a cikin ajujuwan makarantun boko.
Kuma kasa da mako biyu masu zuwa nan gaba ne dalibai za su koma makaranta daga dogon hutu.
Sannan an yi hasashen cewa a nan gaba da sauran dogon lokaci na faduwar ruwan sama.