Nijar za ta haramta shigar da shinkafa nan da 2023

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kuduri aniyar ganin cewa nan da shekara ta 2023 ba a sake shiga da shinkafa kasar ba daga kasashen waje.

Shugaban ya sanar da hakan ne a zaman taro na 19 na kwamitin ministoci mai kula da shiri noma da ake kira Dan _Nijar_Ya Ciyar _Dan _Nijar.

Shi dai wannan tsari an yi shi ne domin samar da wadataccen abinci da 'yan kasar da kansu za su noma domin ciyar da al'umma a fadin kasar baki daya.

Dakta Abubakar Mamman Manzi ne mai bai wa shugaban kasar shawara kan abin da ya shafi sabbin dabarun noma ta hanyar habaka cimaka ya ce za a cimma wannan burin ne ta hanyar yawaita noma shinkafar.

"Za kuma a samar da ruwan da za a dinga amfani da shi wajen noman shinkafar ta yadda za a dinga nomanta sau biyu a shekara, idan aka yi hakan to za a dinga noma tan 15 a shekara a kowace eka," in ji shi.

Sai dai kuma manoman kasar na ganin lamarin zai kasance tamkar kidan ganga da lauje ne, kamar yadda Alhaji Lawali Sa'idu sarkin noma gundumar Gidan Rumji ta jihar Katsinan Maradi ya ce.

"Ban yi mamakin wannan shirin ba, idan har shugaban kasa ya yi niyya ya tsaya tsayin daka yana iyawa, amma mutanen da ke zagaye da shi ne ba su da karsashi.

"Manona za su iya cimma wannan kuduri idan har an ba su tallafi. A Nijar muna da wuraren noma amma babu ruwa, idan dai za a wadata mu da ruwa to ba abin da ya gagari manomi," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Idan shugaban ya dage to ko ba a cimma kudurin a shekarar 2023 ba to za a cimmasa a shekaru masu zuwa."

A shekarar 2010 an shiga tan 257,000 na shinkafa cikin kasar yayin da a bana kuwa aka shiga da tan 426,000.

Jamhuriyyar Nijar ce kasa mafi girman kasa a yankin Afirka Ta Yamma, kuma ta 22 a fadin duniya, sai dai Hamada ce ta lullube kashi 80 cikin 100 na girmanta.

Kasar na yawan mutane miliyan 23,360,695 a kiyasin baya-bayan nan da aka yi.