Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adam A. Zango ya yi hadari a Nijar
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango, ya yi hatsarin mota.
Zango yana tafiya ne a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sai dai jarumin ya ce "Allah Ya kare su, domin hadarin ya tsaya ne kawai a kan motar da suke tafiya a ciki".
Zango yana yawan yin tafiye-tafiye musamman a lokutan bukukuwan sallah, inda ake gayyatarsa domin yin casu.
BBC ta yi kokarin tuntubar A Zango domin neman karin bayani kan lamarin amma bai amsa wayar ba kawo yanzu.
Amma bayanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa ya je Niyami, babban birnin Nijar, domin yin wasan sallah.
Ana dai yawan samun hadari a kan hanyoyin Najeriya musamman a lokutan bukukuwan Sallah ko Kirsimeti.
Masu lura da al'amura na alakanta hakan da rashin kyawun hanyoyi da kuma tukin ganganci daga bangaren wasu matafiyan.