Dan Najeriya na kokarin dawo da kimar Afirka a duniya

Wani matashi dan Najeriya zai fara yawon bude ido domin zakulo matasa 'yan Afirka masu basira da hazaka a fadin duniya.
A lokacin yawon bude idon, Kennedy Ekezie mai shekara 19, zai ziyarci jami'o'i a birane fiye da 20 a cikin wata uku, inda shirinsa mai suna Africave zai samo matasa 'yan Afirka masu basira da nufin dawo da kimar nahiyar a idanun duniya.
Matashin ya shaida wa BBC cewa "Manufar... ita ce ganowa da kuma tara matasan Afirka masu kwazo da basira a fadin duniya a waje daya domin su kawar da kudin goron da ake wa 'yan Afirka."
Kennedy ya kara da cewa shirin Africave ya kunshi gano burikan matasan da "irin gudumuwar da suke so su bayar domin cigaban yankin."
Shirin zai kuma hada matasan da wasu fitattun mutane da gwaraza 'yan Afirka da za su zama abin koyi ga matasan domin su ma su zama gwanayen kansu.
Ekezie ya ce, manufarsa ita ce habbaka basirar 'yan Afirka a bangarorin wasanni da kasuwanci da kungiyoyi masu zaman kansu, kuma duk mai sha'awar bayar da gudumuwa ga ci gaban Afirka zai iya shiga.







