Shin 'yan siyasar Najeriya na ta'azzara labaran bogi?

A

Asalin hoton, Getty Images

Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Yawan 'yan Najeriya masu amfani da shafukan sada-zumunta na ta habaka, musamman saboda arhar da wayoyin China suke da shi da kuma saukin amfani da shafuka kamar WhatsApp da Facebook da sauransu.

WhatsApp ba shi da tsadar amfani sannan Facebook yana da tsarin kyauta da ake kira da "Free Basic".

WhatsApp sananne ne a Najeriya. Kasar tana da mutane mafi yawa masu amfani da shi a fadin Afirka.

Rahoton kamfanin tsare-tsaren kafafen sada zumunta na Hootsuite ya nuna cewa kaso 85 cikin 100 na mutane miliyan 24 da suke amfani da shafukan sada-zumunta suna amfani da WhatsApp, gaba kadan ke nan da Facebook da yake da kaso 78.

A

Asalin hoton, Getty Images

Duk da shafin Twitter yana kara zama sananne amma kaso 30 cikin 100 ne na masu amfani da shi.

Instagram kuwa ya fi zama sananne a hannun mata ne don haka yake da kaso 7.4 cikin 100 kacal.

Kwatankwacin bayanin da 'yan Najeriya ke karba da yada wa a shafukan sada zumunta ya kai girman dakin karatun jami'a a kasar.

Binciken da wasu masana a Jami'ar Nnamdi Azikiwe suka yi, ya nuna cewa mafi yawan matasan kasar suna amfani da shafukan Intanet na kwatankwancin sa'o'i uku zuwa biyar a kowace rana.

Kamar yadda shafukan sada-zumunta suke habaka haka "kamfanonin rudarwa" suke ta bunkasa.

Wannan layi ne

Yaduwa kamar wutar daji

Labaran karya da bayanan shirme da juya gaskiya da ma tsagwaron karya suna ta samun yaduwa a shafukan sada zumunta.

Masu fada-a-ji a shafukan su kansu suna amfani da rashin sanin mutane wajen sake rudar da su don su samu nasarar siyasa.

Binciken hakikar gaskiya kuma sai zama yake wani gagarumin aiki saboda bayanan sun yi yawa kuma sai yaduwa suke akai-akai.

Shafukan tura sakonni kamar WhatsApp suma sun zama wasu dandalin farfaganda, inda ake shiryawa da kirkirar bayanan bogi kuma a sakarwa jama'a domin su hadiya.

Tsofaffin hotuna da labaran karya da kanun labarai mai kunshe da yaudara su ne ke ta yawo a dakunan hira, daga nan kuma a yi ta yada su zuwa shafukan daban-daban.

Da yawan shafukan labarai kuwa sun fi damuwa da 'yan kwabban da za su samu idan an shiga karatu a shafinsu fiye da gaskiyar labaran da suke yadawa.

Wannan babbar matsalar ta shafi siyasar Najeriya ta mummunar hanya.

A

Asalin hoton, Getty Images

Zaben da aka gabatar a shekarar 2019 ya nuna yadda aka yi amfani da shafukan sada-zumunta ta hanyoyin da suka dace da ma wadanda ba su dace ba.

Yayin da masu bincike don gano hakikar gaskiya ke ta aikinsu wajen bayyanawa mutane labaran bogi da za su iya rudar da mutane kuma su iya kai wa ga rigingimun zabe.

Su kam masu sana'ar rudarwa sai ci gaba suka dinga yi wajen yada labaran bogi da suka dinga sanyawa ana tantamar gaskiyar hukumar zabe da kuma sanya fargaba a zukatan 'yan siyasa.

A

Asalin hoton, Getty Images

Yanzu haka jihohin Kogi da Bayelsa za su shiga zaben gwamnonin da ba a yi da su a babban zabe ba.

A irin wannan yanayi ne za a yi ta ganin labaran bogi suna ta yawo.

Kogi a misali, jiha ce da take dauke da mabambanta kabilu da kuma take da tarihin rigingimun zabe.

Tun yanzu an fara ganin alamomin da suke nuna yadda kasuwancin labaran bogi ya gudana a babban zaben da ya gabata.

'Yan siyasa a jihar tuni suka dauki sojojin yada labaran bogi suna yi musu aiki wajen yada bayanan da ka iya rudar da mutane a Intanet.

Wannan layi ne

''Yan siyasa na tunzura yada labaran bogi'

A

Asalin hoton, Getty Images

Wani bincike da Cibiyar Dimokradiyya da Ci Gaba (Centre for Democracy and Development) ta gabatar ya bayyana cewa wasu 'yan siyasar a jihar Kogi suna amfani da shafukan bogi, kai wani lokacin ma na gaske, wajen taimakawa yada bayanan karya.

Amma mafi yawan aikin wasu matasa ne da ake kira da "Data Boys" da kuma "Shekpe Boys" suke yinsa.

Su "Data Boys" su ne masu yi wa jam'iyyar APC da take da gwamnati a hannu aiki.

Ana zargin ana ba su abin da ya kama daga naira 50,000 zuwa 100,000 duk wata domin su yada farfaganda a shafukan sada zumunta.

Su kam "Shekpe Boys" suna bangaran adawa ta PDP ne da ba su fiye samun cikakken taimakon kudi ba saboda rashin gwamnati a hannu.

'Yan siyasa a jihar Kogi sun gane muhimmancin aiki da masu yada labaran bogi.

Wani daga cikin 'yan siyasar da muka tattauna da shi ya bayyana cewa siyasa cike take da farfaganda don haka "wajibi ne dan siyasa ya samu masu taimaka masa a farfaganda idan ba so yake karshensa ya zama irin na Natasha Akpoti ba".

Natasha wata 'yar siyasa ce a jihar da aka dinga yada labaran karya da ake zaton ya kai ga rashin nasararta a zaben kujerar sanata da ta yi takara a watan Febrairun da ya gabata.

Akwai wadanda suke ganin wannan shi ne ya janyo janyewar mata da yawa a fagen siyasar jihar.

Yanzu dai muna zamanin da za a iya kira da na rudarwa saboda tarin bayanai marasa inganci musamman a kafafen sada zumunta.

A yanzu haka rubutu a Facebook, sako a WhatsApp da kuma bayanai a Twitter da suka yi daidai da ra'ayin mutane, ko da na karya ne, suke saurin samun karbuwa.

A kasa irin tamu kuwa da take da bambance-bambancen kabilu da addinai wannan babbar matsala ce.

Wannan layi ne

Mafita

A

Asalin hoton, Getty Images

Duk da dai babu maganin sha-ka-warke na lokaci daya ga wannan babbar cuta ta bayanan bogi, kuma da alamu za a yi ta ci gaba da yakar dimokradiyyar Najeriya ta karkashin kasa da wannan yakin na sunkuru a zabukan kasar da za su yi ta zuwa.

Amma akwai matakan da za a iya dauka wajen dakile wannan matsala.

Kamfanonin shafukan sada zumunta su ya kamata su shigo da sababbin tsare-tsare da za su iya magance wannan matsala musamman ta tsarin manhajojin "Artificial Intelligence" da za su taimaka wajen bibiya da kuma maganin bayanan bogi.

Shafuka kamar Facebook da WhatsApp da Instagram ya kamata su sanya wani maballi da zai dinga kai mai karatu ga asalin sako.

Wannan zai sanya a gane shin labarai suna da tushe ko babu.

Ilimin fasahar bayanai (Digital Literacy) kuwa ya kamata ya shiga cikin manhajojin ilimi a Najeriya, domin duk abin da na'uori za su yi sai da sa hannun mai amfani da su wajen ingancinsu.

A shigar da ilimin tunani mai zurfi cikin manhajojin ilimi tun daga tushe tun da dai Najeriya tana ta bunkasa fasahar bayananta.

Wannan shi zai sanya duk mai amfani da kafafen sada zumunta ya dinga karanta labarai ba kanunsu kawai ba, ya nemo tushen bayanin don aunawa, ya nemo wasu bayanan da ka iya taimakawa wajen karfafawa ko rage karfin wanda ya gani.

Hakazalika ya duba tarihi da kwanan watan bayanin da ya gani; sannan ya tabbatar ba zambo ba ne kafin ya tabbatar da gaskiya ko rashin gaskiyar bayanin.

Aliyu Dahiru Aliyu jami'in shirye-shirye ne kuma mai bincike akan labaran bogi a Najeriya da yake aiki da Cibiyar Dimokradiyya da Ci Gaba (Centre for Democracy and Development) a Abuja, Najeriya.