Al'amura sun tsaya cik a Kashmir

Asalin hoton, Getty Images
Al'amura sun tsaya cik a yankin Kashmir na India na, tun bayan da gwamnatin India din ta sauya matsayi kan yiwuwar samun 'yancin yankin daga India.
A ranar Lahadin da gabata ne dai aka yanke hanyoyin sadarwa da suka hada da waya da intanet kuma har yanzu ba su dawo ba, a dai-dai lokacin da dubun dubatar jami'an tsaron kasar ke sintiri a kan titunan yankin.
An samu yanayin da masu zanga-zanga suke jefe-jefen duwatsu duk da matsalar yankewar hanyoyin sadarwar da kuma dokar hana zurga-zurga. An kuma kama da tsare shugabannin yankin.
India da Pakistan dai na ikrarin mallakar lardin Himalayan na yankin Kashmir duk da cewa kowacce daga cikin kasashen biyu na iko da wani bagare ne na lardin.
A bangaren Kashmir din na India, an kwashe lokaci mai tsawo ana samun tayar da kayar baya al'amarin da ya haddasa rasa rayukan dubban jama'a a fiye da shekaru 30.







