Mun kama Sowore kan yunkurin kifar da gwamnati - SSS

Asalin hoton, Sahara Reporters
Jami'an hukumar tsaron ta farin kaya wato SSS, yayin wani taron manema labarai da suka yi a Abuja, ranar Lahadi, sun ce sun kama Omoyele Sowore, mai kamfanin jaridar Sahara Reporters ta intanet kan shelar da ya yi ta #RevolutionNow da ke nufin juyin juya-hali.
Mai magana da yawun hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya, ya ce suna da cikakkiyar masaniya kan 'goyon bayan' da Mista Sowore yake samu daga kasashen waje da nufin tayar da tarzoma a Najeriya ta hanyar shelar da ya yi ta 'samar da sauyi a kasar'.
Sai dai jami'in hukumar bai fadi ko yaushe ne za a gurfanar da mista Sowore a gaban kotu ba.

Da safiyar Asabar din da ta gabata ne dai 'yan uwa da abokai da mabiyan mai kamfanin jaridar Sahara Reporters ta Intanet, Omoyele Sowore suka zargi jami'an tsaron hukumar DSS da kame dan uwan nasu.
Omoyele Sowore dai wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya a babban zaben 2019 a jam'iyyar AAC ya yi shelar jama'a su fito domin juyin juya-hali a kasar daga ranar Litinin din mako mai kamawa da manufar kawo sauyi dangane da yadda al'amura suka tabarbare.
Da misalin karfe 1:25 na daren Juma'a Omoyele ya wallafa a twitter cewa jami'an DSS sun shiga gidansa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Batun yana tashe a Soshiyal Midiya
Batun bacewar da Sowore ya yi da kuma zargin jami'an hukumar SSS da kama shi ya zama babban batu a ranar Asabar a shafukan sada zumunta musamman twitter. Tuni mutane suka kirkiri wani maudu'i na neman a saki dan jaridar wato '#FreeSowore'.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wannan na cewa 'yan Najeriya na neman a saki Sowore. Zanga-zanga ai ba garkuwa da mutane ba ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Shi kuma wannan yana fadin cewa yin zanga-zanga 'yancin dan adam ne a duk duniya saboda suke neman shugaba Buhari 'ya saki' Sowore ba tare da bata lokaci ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Sai wannan da yake gama shugaba Buhari da Allah da ya 'saki' Sowore.

#RevolutionNow
A farkon makon da ya gabata ne dai mai kamfanin jaridar ta Sahara Reporters ya fito da maudu'i a kafafen sada zumunta na #RevolutionNow domin yin zanga-zangar matsa wa gwamnatin Muhammadu Buhari lamba ta gyara zamanta.
Rahotanni sun ce wasu kungiyoyi masu fafutukar yaki da rashawa da cin hanci da kuma na kare hakkin dan adam kamar Amnesty International sun 'kwarara wa' masu son yin juyin juya-halin gwiwa.
Hakan ne ya sa a ranar Alhamis fadar shugaban Najeriya ta fito da wata sanarwa inda ta ce duk abun da ya faru a kasar to ta dora alhakin hakan kan kungiyar Amnesty International.
A ranar Juma'a kuma an samu gomman 'yan Najeriya da suka yi dandazo a kofar ofishin kungiyar ta Amnesty da ke Abuja domin yin zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu ga 'goyon bayan' da aka ce kungiyar ta bai wa masu son yin juyin juya-halin.
To sai dai kungiyar Amnesty International a wata sanarwa da ta aike wa da BBC ta ce "aikinta shi ne sa ido kan tabbatar da kare hakkokin bil'adama ba siyasa ba."
Sanarwar ta kara da cewa "tun 1967 Amnesty International take aiki - na tunatar da gwamnatoci kan kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da cewa duk wanda aka zalunta an bi masa hakkinsa."
"Saboda haka, kungiyar Amnesty za ta ci gaba da kira ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta gudanar da bincike kan zarge-zargen cin zarafin bil'adama da suka hada da fyade, azabtarwa, tsarewa da kisan mutane ba bisa ka'ida ba." In ji sanarwar
Daga karshe Amnesty ta ce "Duk da mutanen da gwamnati take biya su yi wa kungiyar zanga-zanga, to ba za mu yi shiru ba. Kuma za mu ci gaba da bankada rashin adalci da cin zarafi da nuna wa mata banbanci da duk wani nau'in danne wa 'yan Najeriya hakkokinsu a duk inda muka ga ana yi."
'Yan sanda sun ce zanga-zangar ta'addanci ce

Asalin hoton, Facebook
Sifeton 'yan sandan, Muhammad Adamu a wani gargadi da rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na twitter, ya ce rundunar 'yan sanda ba za ta zura ido ga masu son kifar da zababbiyar gwamnati ba.
Gargadin ya ce "rundunar 'yan sanda ta ga wani bidiyon da ke karakaina a soshiyal midiya wanda ya fito daga wata kungiya mai suna Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria and others', da ke tunzura 'yan Najeirya na gida da waje wajen shiga a dama da su a zanga-zangar yi wa gwamnatin Najeriya matsin lamba a ranar Litinin 5 ga watan Agusta da manufar kifar da gwamnatin."
Rundunar da ta kara da cewa " Rundunar 'yan sanda na sanar da jama'a ba tare da shakku ba cewa wannan zanga-zangar daidai take da cin amanar kasa da aikin ta'addanci saboda haka rundunar ba za ta zura wa masu yunkurin yin hakan ido ba su tayar da zaune tsaye a kasa ba."
Sifeto Janar ya kara da cewa "a dai-dai lokacin da wasu ke yin amfani da 'yancinsu na yin zanga-zangar lumana, rundunar 'yan sanda na son sanar da su cewa bai kamata 'yancin nasu ya janyo rikici ba ko kuma ya kifar da gwamnati wanda ma'anar 'revolution ke nan."