LGBT: Murnar 'yan luwadi ka iya komawa ciki a Botswana

Gwamantin Botswana za ta daukaka kara ta neman sauya hukuncin da ya hana yi wa 'yan luwadi hukunci a kasar wanda wata babbar kotu ta yanke, in ji ministan shari'ar kasar.
A watan da ya gabata ne dai kotun ta yi watsi da tanade-tanaden dokokin kasar na zamanin turawan mulkin mallaka da suka tanadi daurin shekara bakwai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin yin luwadi ko madigo.
Kotun dai ta kafa dalilin cewa tanade-tanaden sun yi karo da tsarin mulkin kasar.
Wasu dai na yi wa hukuncin kallon wani mataki na kokarin bai wa 'yan luwadi da madigo 'yanci a Afirka.
To sai dai ministan Shari'ar kasar ta Boswana, Abraham Keetshabe ya ce alkalan da suka yanke hukuncin sun 'tafka kuskure'.
A wata sanatwa da ya fitar ranar Juma'a Abraham Keetshabe ya ce "na karanta hukuncin mai shafi 132 kuma na yi imanin cewa babbar kotun ta yi kuskure wajen ynake hukuncin."
Ya kara da cewa zai daukaka kara amma bai yi karin haske dangane da hurumin karar ba.
A ranar 11 ga watan Yunin 2019 ne dai kotun ta yanke hukuncin hana daukar mataki kan masu luwadi da madigo, bayan da bakin alkalai uku ya zo daya.
Alkalan dai sun ce hukunta masu neman jinsi guda 'nuna wariya ne' kasancewar yana yin halitta ne a jikin masu yin.
Wani dalibi ne dai ya shugar da karar yana neman a goge dokokin kasar da suka tanadi hukunta masu luwadi da madigo.
Tuni dai kasashen Angola da Mozambique da Seychelles suka halasta luwadi da madigo ta hanyar soke dokokin da suka tanadi hukunta masu yi.
To sai dai a kasashen Afirka kamar Sudan da Somalia da Mauritania da Najeriya luwadi laifi ne abin hukuntawa.
A arewacin Najeriya ma hukuncin kisa ne ga duk mutumin da aka kama da luwadin.
A watan Mayu ne wata babbar kotu a kasar Kenya ta yi watsi da wani yunkurin soke dokar da ta halasta luwadi a kasar.











