Me ya sa Larabawa ke juya wa addinin Musulunci baya?

Ana samun karuwar Larabawan da ke barin addinin musulunci kamar yadda wani gagarumin bincike da aka gudanar a Gabas Ta Tsakiya da Arewacin Afirka ya nuna.
Sakamakon binciken ya yi nuni kan tunanin Larabawa dangane da abubuwa da dama da suka hada da 'yancin mata da kaura da tsaro da kuma neman jinsi guda.
An ji ta bakin fiye da mutum 25,000 a yayin binciken - wanda Sashen Larabci na BBC News da cibiyar bincike ta Arab Barometer suka yi a kasashe 10 na Larabawa da Yankunan Falasdinawa daga 2018 zuwa 2019.
Ga dai wasu daga cikin sakamakon binciken:

Tun shekarar 2013 yawan mutanen da ake ganin ba su da addini ya karu daga kashi 8% zuwa kashi 13% a cewar binciken. A Yemen ne kawai ba a samu karuwar hakan ba.

Mutane da dama a yankin suna goyon bayan a bai wa mata damar su zama firaminista ko shugabar kasa.
A Aljeriya ne kawai ba a samu hakan ba inda kasa da kashi 50% na wadanda aka tambaya suka yi amannar cewa za su yarda da mace shugabar kasa.
Amma idan aka zo batun harkokin gida, mutane da dama da suka hada da mata - sun yi amannar cewa miji ne ke da ta cewa a dukkan harkokin da suka shafi iyali.
A Moroko ne kawai mutane kadan suka yarda cewa miji ne yake da dukkan ikon yanke kowane irin hukunci a cikin iyalin.

Luwadi bai samu karbuwa ba a yankin kasashen Larabawa. A Lebanon, duk da cewa akwai sassaucin ra'ayi a can fiye da makwabtanta, adadin masu wannan akida kashi 6% ne.
Kisan wadanda suka ja wa danginsu abin kunya shi ne yadda ake samun iyali su kashe daya daga cikin danginsu musamman mace, saboda jawo musu abin kunya.

A binciken da aka gudanar a ko ina - sakamakon ya nuna cewa ba a maraba da manufofin Donald Trump idan aka kwatanta shi da Shugabanni biyu na Turkiyya da na Rasha.
A bakwai daga cikin wurare 11 da aka yi binciken, rabi ko fiye da haka sun fi yarda da manufofin shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Lebanon da Libiya da Masar sun fi amince wa da manufofin Vladimir Putin na Rasha fiye da na Erdogan.

Jumullar adadin kowace kasa ba 100 bisa 100 ba ne ko yaushe saboda akwai wadanda ba su da zabi da ba a sa a ciki ba.
Tsaro ya kasance daya daga cikin abubuwan da aka damu da su a Gabas Ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
Da aka yi musu tambaya a kan cewa wace kasa ce ta fi zama barazana ga zaman lafiya da tsaronsu, Isra'ila ce ta zo ta farko, sannan sai Amurka, sai kuma Iran da ta zo ta uku.

A duk inda aka yi tambaya, bincike na nuna cewa akalla daya daga cikin mutum biyar na son yin kaura.
A Sudan, rabin 'yan kasar ke da wannan burin.
Dalilai kamar na tattalin arziki na daga cikin abin da ke janyo hakan.
Wadanda aka tambaya na iya zabar fiye da zabi daya. Idan kun kasa kallon taswirar da ke sama, ku latsa nan.
Yawan wadanda suke son barin Arewacin Afirka ya karu, duk da cewa an rage son zuwa Turai, har yanzu dai ita ce a kan gaba na zabin mutanen da ke son barin yankin.
Daga Becky Dale da Irene de la Torre Arenas da Clara Guibour da kuma Tom de Castella.
Sashen Larabci na BBC za su yi ta tattauna wannan batun cikin makon nan. Kuna iya bin #BBCARABICSURVEY a Twitter da Facebook da Instagram don karin bayanin.

Hanyar da aka bi wajen bincike
An gudanar da binciken ne tare da hadin gwiwar wata cibiyar bincike ta Arab Barometer. A yayin aikin an ji ta bakin mutum 25,407 ta hanyar hira da su gaba da gaba a kasashe 10 da Yankunan Falasdinu.
Cibiyar Arab Barometer wata cibiyar bincike ce da take Jami'ar Princeton. Tun shekarar 2006 suke gudanar da bincike. Masu bincike ne suka gudanar da hirar, wacce take daukar tsawon minti 45 a wasu wurare na sirri.
Abu ne da ya shafi ra'ayin Larabawa, don haka bai shafi Iran da Isra'ila ba duk da cewa ya shafi mazauna Yankunan Falasdinu. An saka yawancin kasashen yankin a ciki amma mafi yawan gwamnatocin kasashen yankin Gulf sun ki bayar da hadin kai wajen aiwatar da binciken.
Sakamaon kasar Kuwait bai iso da wuri ba don haka BBC Arabic ba ta sa shi ciki ba. Ita kuma Syria ba a samu shigarta ba saboda wahalar da ke tattare da shiga kasar.
Wasu kasashen sun ce a cire wasu tambayoyin saboda batu na shari'a da al'ada. Ana sanar da hakan a cikin sakamakon.
Za ku iya samun karin bayani a kan hanyoyin da aka bi wajen yin binciken a adireshin intanet na Arab Barometer.












