Abubuwa biyar game da Yariman Saudiyya mai jiran gado

Asalin hoton, Getty Images
Wakilin BBC kan sha'anin tsaro Frank Gardner ya duba yanayi da salon tafiyar Yariman mai jiran gado tun bayan kara masa karfin iko.
1.Matashi
Muhammad Bin Salman matashi ne dan shekara 32, wanda nauyin tafiyar da gwamnati ya yi ma sa yawa.
Shi ne Ministan tsaro da tattalin arziki. Ya kai ga wannan matsayin ne saboda daukakar da ya samu daga mahaifinsa Sarkin Saudiyya, Salman.
2.Ya sa an kame Ministoci da Yarimomin Saudiyya
Tuni aka fara danganta shi a matsayin mai karfin iko, inda a ranar 4 ga watan Nuwamba Yariman mai jiran gado ya bayar da umurnin a kama ministoci hudu da yarimomin gidan sarautar Saudiyya wadanda aka kargame tare da karbe kadarorin da suka mallaka, abin da ba a taba gani ba a Saudiyya.
Mutanen dai wadanda sanannu ne a Saudiyay sun kunyata a idon duniya bayan zarginsu da aka ce an yi da cin hanci da rashawa.
Yayin da wasu ke ganin yarfen siyasa ce kawai daga Yariman mai jiran gado domin karawa kansa karfin iko.
3.Yana son mata su yi tukin mota
Yariman mai jiran gado ya kasance cikin masu karfin fada aji kalilan a kasa irin Sadiyya da ke bin tafarkin addini da suka ga lokaci ya yi a ba mata 'yancin tukin mota.
Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da 'yancin tuki, amma ana fatar samun sauyi a watan Yunin 2018, lokacin da dage haramcin zai soma aiki.
4.Diba hanyoyin rage dogaro da arzikin man fetur
Yariman na kokarin bin wasu sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Saudiyya domin rage dogaro da arzikin Mai da ake ganin wata rana zai iya karewa.
Kan wannan bukatar ne ya kaddamar da wani sabon shiri da ake kira Vision 2030, wato sabbin manufofi da ake fatar cimma, da suka shafi ci gaba a fannin fasaha, kamar kera motoci da jirage masu tuka kansu da samar da wuraren shakatawa kamar Silma, wato wajen nuna finafinai, abin da ba a taba gani ba a kasa irin Saudiyya.
Kuma duk wani da ya nemi kalubalantar manufofin Yariman zai tabbatar cewa an tube shi.
5.Ya shiga yaki da dama
Yariman Saudiyyan mai jiran gado na yaki da makiya a lokaci daya, inda a shekaru fiye da biyu ya jefa dakarun kasar yaki a Yemen, yakin da har yanzu babu nasara wanda ya janyo kashe makudan kudi da tagayyara daruruwan mutane a Yemen.
Sannan Yariman ne ya haddasa rikicin Qatar tsakaninta manyan kasashen tekun Fasha, wanda yanzu haka ke tasiri ga tattalin arzikin kasashen.
Yarima na da hannu sosai a yakin cacar-baka da Saudiyya ke yi da Iran, inda dukkanin kasashen biyu ke zargin juna da talakar yaki da kuma zama sanadin jefa yankin gabas ta tsakiya halin da ya ke ciki a yanzu.











