Elisha Abbo: Atiku ya sa baki kan batun cin zarafin wata mata

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Atiku ne dan takarar PDP na shugaban kasa a babban zaben 2019
Lokacin karatu: Minti 2

Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa a kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan bidiyon nan da ya karade shafukan sada zumunta, wadda wani sanata ya doke wata mai jiran shago.

Jaridar Premium Times ce dai ta wallafa bidiyon da ta yi ikirarin cewa Sanata Elisha Abbo ne yake marin wata mai jiran shagon sayar da kayan jima'i na roba a birnin Abuja.

Tun bayan haka ne kuma 'yan Najeriya suke bayyana rashin jin dadinsu da kuma kiraye-kirayen da a hukunta sanatan a shafukan sada zumunta.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Alhaji Atiku Abubakar wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a babban zaben 2019, ya ce ya yi wa sanatan farin sani amma kamata matasan shugabanni irinsa su zama abin koyi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya kara da cewa ya kamata sanatan ya mika kansa ga 'yan sanda.

"Ina shawartarsa da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga 'yan sanda domin ya nuna dattako," Atiku ya fada.

A wani sakon daban kuma, ya ce ya kamata jam'iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan.

"Ina kira ga uwar jam'iyyarmu ta PDP da ta dauki matakin ladaftarwa a kansa, su ma 'yan sanda su tabbatar cewa doka ta yi aikinta."

Sanata Elisha Abbo dai yana wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa ne a majalisar dattawa, kuma wannnan shi ne karon farko da ya je majalisar.

Sanatan mai shekara 41 yana cikin 'yan majalisar dattawa mafi kankantar shekaru a majalisar.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara binciken Sanata Elisha Abbo wanda ake zargin ya ci zarafin wata mata a kantin sayar da robobin jima'i a Abuja.

Mai magana da yawun rundunar Frank Mba ya shaida wa BBC cewa Babban Sufeton 'yan sandan kasar Muhammed Adamu ya bayar da umarnin a fara binciken dan majalisar dattawan.