An kama matafiya da kunkuru sama da 5,000 a filin jirgi
Mahukunta a kasar Malaysia sun gano kunkuru har 5,000 a cikin wata jaka a filin jirgin sama na Kuala Lumpur, inda nan take suka kwace su.
An tsare wasu 'yan kasar Indiya guda biyu bayan an gano gungun kunkurun - masu jan kunne kuma wadanda ke iya rayuwa a waje da kuma cikin ruwa - a cikin wasu kwanduna kunshe a cikin jakunkunansu.
Mahukuntan sun ce gungun kunkurun ya kai kimar kudi dala $12,700, kuma an yi yunkurin safararsu ne zuwa kasar Indiya.
Malaysia ta zama matattarar masu safarar dabbobi wadanda ake kai su kasashen Asiya.
An kama mutum biyun ne a makon da ya gabata bayan sun isa Kuala Lumpur daga birnin Guangzhou na China, kamar yadda babban jami'in hukumar kwastam Zulkurnain Mohamed Yusof ya bayyana.
Mutanan masu shekaru 30 zuwa 42 ba su da izinin mallakar kunkurun, in ji shi, kuma yanzu za su iya fuskantar daurin shekara biyar a gidan yari.
"Wannan ne karon farko da muke ganin irin wannan laifin kuma ba za mu iya tabbatarwa ko ya kai girman abin da muka saba gani ba.
"Amma da alama kunkurun da yawansu ganin yadda aka same su cikin akwati biyu a lokaci guda," Mista Yusof ya shaida wa taron manema labarai a ranar Laraba.
Kunkuru masu jan kunnne su ne aka fi kauna a kasuwar dabbobi masu shiga rai wato pet a Turance, in ji kungiyar International Union for the Conservation of Nature - kungiya mai kula da yanayi.
Ana ganin su a matsayin dabbobi masu yaduwa a kankanin lokaci sannnan kuma ana samun su yanzu a kasashe da yawa saboda wasu iyayen gidansu sun sake su ko kuma sun tsere.
Kunkurun da aka kwace a Malaysia za a mayar da su karkashin kulawar hukumar kula da namun daji ta kasar.












