Afcon 2019: Yadda wasan Najeriya da Guinea ke kasancewa

Nigeria vs Guinea match result

Asalin hoton, GIUSEPPE CACACE

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta zama ta farko da ta kai zagayen gaba a gasar cin Kofin Kasashen Afirka da ake yi a kasar Masar.

Super Eagles ta yi nasara ne a kan Guinea da ci daya mai ban haushi a wasa na biyu na rukuni na biyu da suka fafata a Alexandria.

Najeriya ta ci kwallon ne ta hannun Kenneth Omeruo a minti na 73.

Da wannan sakamakon Najeriya ta hada maki shida a wasa biyu, bayan da ta ci Burundi 1-0 ranar Asabar.

Najeriya za ta buga wasa na uku da Madagascar ranar Lahadi 30 ga watan Yuni a filin wasa na Alexandria.

Ita kuwa Guinea tana da maki daya a wasa biyu ne, bayan da ta tashi 2-2 da Madagascar a ranar Asabar a karawar rukuni na biyun.

Sakamakon wasa

Nigeriya 1
-
0 Guninea
An tashi wasa
Karin bayani game da wasan
Salon wasa
Nigeriya
(4-2-3-1)
Guninea
(4-2-3-1)
Karin bayani game da wasan
  • 27
    -
    Falette
    0 - 0
  • 62
    -
    Musa
    0 - 0
  • 65
    -
    Seka
    0 - 0
  • 71
    -
    Naby Keita
    down
    Lass
    up
    0 - 0
  • 73
    -
    Dyrestam
    down
    Sidibé
    up
    0 - 0
  • 73
    -
    Omeruo
    football
    1 - 0
  • 78
    -
    Iwobi
    down
    Chukwueze
    up
    1 - 0
  • 82
    -
    Kamano
    down
    Koita
    up
    1 - 0
  • 88
    -
    Ighalo
    down
    Paul Onuachu
    up
    1 - 0
  • 90
    -
    Peter Etebo
    1 - 0
  • 94
    -
    Simon
    down
    Kalu
    up
    1 - 0
Alkalumman wasa
Nigeriya
Guninea
  • Yawan rike kwallo
    48.2%
    51.8%
  • Harin da ya nufi raga
    4
    3
  • Kai hari daga nesa
    10
    8
  • Bugun kwana
    10
    1
  • Keta
    13
    12
Jerin 'yan wasan da za su buga wasa
Yan wasan da za su fara taka leda
Nigeriya
  • 16
    Akpeyi
  • 22
    Omeruo
  • 6
    Balogun
  • 2
    Ola Aina
  • 20
    Awaziem
  • 4
    Wilfred Ndidi
  • 7
    Musa
  • 15
    Simon
  • 8
    Peter Etebo
  • 18
    Iwobi
  • 9
    Ighalo
Guninea
  • 12
    Koné
  • 3
    Issiaga Sylla
  • 18
    Dyrestam
  • 5
    Seka
  • 6
    Falette
  • 10
    Kamano
  • 13
    Cissé
  • 4
    Diawara
  • 16
    Traoré
  • 8
    Naby Keita
  • 21
    Kaba
Canji
  • 78
    Iwobi
    down
    Chukwueze
    up
  • 88
    Ighalo
    down
    Paul Onuachu
    up
  • 94
    Simon
    down
    Kalu
    up
  • 71
    Naby Keita
    down
    Lass
    up
  • 73
    Dyrestam
    down
    Sidibé
    up
  • 82
    Kamano
    down
    Koita
    up
Masu jiran benci
  • 10
    Mikel
  • 5
    Troost-Ekong
  • 11
    Onyekuru
  • 19
    Ogu
  • 17
    Kalu
  • 21
    Osimhen
  • 23
    Uzoho
  • 1
    Ezenwa
  • 13
    Chukwueze
  • 14
    Paul Onuachu
  • 9
    Kanté
  • 2
    Mohamed Yattara
  • 7
    Mohamed Camara
  • 23
    Fodé Camara
  • 19
    Koita
  • 11
    Idrissa Sylla
  • 17
    Fofana
  • 20
    Lass
  • 1
    Naby-Moussa Yattara
  • 14
    Sidibé
  • 22
    Aly Keita
  • 15
    Jeanvier
Nigeria vs Guinea match result

Asalin hoton, GIUSEPPE CACACE

Guinea za ta fafata da Burundi ranar Lahadi 30 ga watan Yuni a wasa na uku na cikin rukuni na biyu.

A ranar Alhamis 27 ga watan Yuni ne Burundi za ta kara da Madagascar a daya wasa na biyu a rukuni na biyu a Alexandria.

Takaddama

'Yan wasan Najeriya na takaddama da hukumar kwallon kafar kasar tun kafin wannan karawa da za ta yi da Guinea a gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Laraba.

Kawo yanzu babu wani dan wasan Super Eagles da ya karbi alawus ko kuma ladan wasa na dala dubu 10.

Hukumar kwallon kafa ta NFF, na fatan kamo bakin zare ka da 'yan wasa su ki fita fafatawa da Guinea ranar Laraba a Masar.

Sai dai 'yan wasan sun janye kauracewa wasan Guinea, inda suka fito wasan gadan-gadan.

Kocin Najeriya, Gernot Rohr ya ce ''Dalilin da ya sa Ahmed Musa bai halarci taro da 'yan jarida ba ranar Talata, saboda 'yan wasan suna da wani taro a tsakaninsu mai mahimmanci."

Gernot Rohr

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kocin Super Eagles Gernot Rohr ya karbi tawagar ne a 2016

'Yan wasan sun makara zuwa atisaye na sa'a daya ranar Talata, kuma suna shirin daukar wasu matakin.

NFF, wadda take karbar kudin bukatunta daga gwamnati ta musanta zargin da ake mata cewar ita ce ta kawo tsaikon biyan alawus-alawus da ladan buga kwallo.

BBC ta fahimci cewa tawagar kwallon kafa ta Najeriya wadda suke tare tun watan Yuni, an yi mata alkawarin baki cewar za a biya su hakkinsu kafin fara gasar kofin nahiyar Afirka.

Wannan ba shi ne karo na farko da 'yan wasan Super Eagles ke kin zuwa atisaye ba, sakamakon kin biyan hakkinsu a lokacin wasu manyan wasannin tamaula.

A gasar cin kofin duniya da aka yi a 2014, 'yan wasan Najeriya sun ki zuwa atisaye kan rashin biyansu hakkinsi, a wasan zagaye na biyu da za ta fafata da Faransa.

Tawagar kwallon kafa ta Mata ta Nijeriya, Super Falcons ta yi bore karo biyu inda ta fara a Afirka ta Kudu da zuwa Abuja kan biyan hakki.

Haka kuma Super Falcons ta nemi hakkinta bayan da aka fitar da kasar a gasar cin kofin duniya a Faransa.