Da gaske gwamna ya boye bindigogi kirar AK47?

Makaman na daban dai an same su a hannun tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun
Bayanan hoto, An dade ana nuna damuwa kan yawaitar makamai a hannun jama'a a Najeriya
Lokacin karatu: Minti 3

Batun boye makamai da suka hada da AK47 1,000 da wata jarida a Najeriya ta ce tsohon gwamnan Ogun ya yi na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

Kafar yada labarai ta Premium Times ce ta rawaito cewa tsohon gwamnan, Sanata Ibikunle Amosun ya boye dimbin bindigogi kirar AK47 da harsasai miliyan hudu na tsawon lokaci ba tare da sanin jami'an tsaro ba.

Rahoton jaridar ya ce a ranar 28 ga Mayu, 'yan sa'o'i kafin mulkinsa na shekaru takwas ya kawo karshe, sannan ya kira kwamishin 'yan sandan jihar ya mika masa makaman a gidan gwamnati.

Sai dai kuma tsohon gwamnan ya musanta rahoton inda wata sanarwa da mai magana da yawunsa Rotimi Durojaiye ya aikewa BBC ya ce Premium Times ta murda gaskiyar yadda labarin yake.

Ya ce ya yanke shawarar ajiye makaman ne a gidan gwamnatin don tabbatar da cewa jami'an tsaron ba su yi wasa da makaman ba.

Ya kuma ce tsohuwar gwamnatin ta ware kudi domin sayan makaman da suka hada da motocin yaki 13 da bindigogi AK47 1,000 da riga da huluna masu sulke 1,500 da harsasai miliyan biyu.

Sanarwar ta ce kowa ya san matsalolin tsaro da jihar Ogun ta yi fama a shekarun baya da suka hada da garkuwa da mutane da kashe-kashe da tashin hankali, wani abu da ya tilastawa gwamnatinsa daukar matakin da ya dace.

"Ba a sayo makaman ba sai da amincewar fadar shugaban kasa a zamanin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan," in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa bisa tsari dai kowacce fadar gwamnatin jiha na tanadin makamai domin kare yankinta.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya, musamman ma a kafofin sadarwa na Intanet, inda wasu ke cewa tarin makamai kamar wannan kamata ya yi ace suna a hannun hukumar tsaro ta cikin gida ba gwamna ba ko wani dan siyasa ba.

Wasu na nuna alamar tambaya kan lokacin da aka dauka makaman na ajiye tun lokacin da gwamnan ya ce ya sayo a 2012 da kuma yadda sai a 2019 aka mika wa 'yan sanda.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Rahoton Premium Times ya nuna shakku ne kan ko gwamna yana da 'yancin ajiye makamai da aka sayo har sai zuwa lokacin da zai mika mulki.

Sai dai wasu sun kalubalanci rahoton jaridar, yayin da wasu kuma suka nuna rashin gamsuwa da yadda tsohon gwamnan ya kare kansa.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Ogun Bashir Makama ya shaida wa BBC cewa abin da ya sani shi ne harsashe miliyan daya da dari biyu ne tsohon gwamnan ya mika wa rundunarsu amma ba miliyan hudu ba.

Ya kara da cewa akwai yiwuwa tsohon gwamnan ya mika bindigogin a baya kafin ya kama aiki a jihar.

Ya ce tun farko ya fadawa gwamnan cewa abokan hamayya suna zarginsa da mallakar makamai, zargin da ya musantawa kwamishinan na 'yan sandan.

Dama dai ana zargin wasu daga cikin 'yan siyasa cewa suna raba makamai ga 'yan baranda domin kare muradunsu.