Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ba ku sani ba kan sabon shugaban NNPC
Ranar 20 ga watan Yunin 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kolo Kyari kuma magajin Maikanti Baru.
A watan Yuli ne dai ake sa ran Maikanti Baru zai yi ritaya daga matsayinsa a kamfanin na NNPC.
Mele Kyari dai ya kwashe shekaru yana aiki a kamfanin na NNPC inda ya rike mukamai daban-daban.
An haifi Mista Kyari ranar 8 ga watan Janairun 1965 a Maiduguri, jihar Barno kuma ya yi makarantar sakandare a Government Community Secondary School da ke Biu a jihar ta Borno daga shekarar 1977 zuwa ta 1982.
Daga nan ne ya tafi jami'ar Maiduguri inda ya yi digirinsa a fannin nazarin duwatsu da albarkatun kasa kuma ya kammala a shekarar 1987.
Ya yi bautar kasa da Hukumar samar da Abinci da More rayuwa ta DFRRRI tsakanin shekarar 1987 da ta 1988.
Ya kwashe sama da shekara 32 a masana'antar man fetur da iskar gas kuma aikinsa ya kewaya da shi bangarori da dama na masana'antar, kuma ya rike mukamai da dama a ciki da wajen NNPC.
Ya taba rike mukamin babban jami'i mai kula da ayyukan bangaren zuba hannun jari a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya, NAPIMS kuma ya taba zama mai kula da bangaren sayar da danyen man fetur na kamfanin NNPC.
A cewar NNPC, karkashin jagorancinsa, bangaren sayar da danyen man fetur na kamfanin ya ga manyan sauye-sauye a yadda ake tafiyarwa da siyar da azuzuwan danyen mai ta kirkirar sahihai da ingantattun hanyoyi.
Mele Kyari ya sha karbar kyaututtuka da lambobin yabo a bangaren aikinsa.
A shekarar 2007 ya ci kyautar shugaban NNPC ta ma'aikacin da ya fi ko wanne kwazo da kuma lambar yabo ta GEDCS a fannin shugabanci.
A shekarar 2018 ne aka nada Mista Kyari wakilin Najeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC.
Sannan ya zamo ya zamo shugaban kamfanin NNPC na 19.
Jerin shugabannin kamfanin NNPC na da:
- Cif R.A Marinho
- Cif Odiligi Lolomari
- Mista Lawrence Amu
- Mista Aret Adams
- Dakta Thomas John
- Mista Edmund Dauoru
- Cif Chamberlin Oyibo
- Alh. Dalhatu Bayero
- Dakta Jackson Gaius Obaseki
- Farfesa Funsho Kupolokun
- Abubakar Yar'Adua
- Muhammed Sanusi Bakindo
- Shenu Ladan
- Augustine O. Oniwon
- Mr. Andrew Yakubu
- Ibe Kachukwu
- Dakta Maikanti Baru