Hotunan bikin ranar demokradiyya a Najeriya
Najeriya ta yi bikin ranar Demokradiyya ran 12 ga Yuni, don tunawa da sahihin zabe na farko da aka fara yi a kasar ran 12 ga watan Yunin 1993, shekaru goma bayan mulkin soja.
Ga wasu daga cikin hotunan abubuwan da suka faru a lokacin bikin.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari da Mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa Dolapo Osinbajo da sabon Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da sauran manyan baki a wajen bikin.

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin masu nishadantar da mutane a lokacin da take taka rawa a Dandalin Eagle Square da ke birnin Abuja.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a lokacin da ake tuka shi a mota inda ya ke duban masu faretin girmamawa a Dandalin Eagle Square.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron bikin ranar demokradiyyar har da 'yan kasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images
Faretin 'yan sanda a lokacin bikin ranar demokradiyya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yana gaisawa da shugaban Rwanda Paul Kagame a lokacin bikin. Daga bayansu kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya ne Ken Nnamani da wasu manyan baki.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu sojoji suna fareti a gaban Shugaba Muhammadu Buhari yayin da shi kuma yake kallonsu a Dandalin Eagle Square a lokacin bikin.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Wasu 'yan rawa suna nishadantar da 'yan kallo a filin da aka gudanar da bikin a Abuja.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake jawabi a Dandalin Eagle Square.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar adamu yana sara wa Shugaba Muhammadu Buhari.











